logo

HAUSA

Martaba rayuka ita ce yadda ake rungumar manufar “Dakile cutar Covid-19 da zarar an gano ta”

2022-04-14 14:27:52 CMG Hausa

Har yanzu cutar Covid-19 na ci gaba da yaduwa a sassan duniya. A nan kasar Sin, cutar nau’in Omicron ta bulla a larduna 30 na kasar tun daga watan Maris, inda aka ba da rahoton mutane sama da dubu 320 sun harbu da cutar. A yayin fuskantar saurin yaduwar cutar, gwamnatin kasar Sin ta jaddada rungumar babbar manufarta ta “dakile cutar da zarar an gano ta”, wadda ta bayyana yadda kasar ke dora al’ummarta da ma rayukansu a gaban kome.

Kasar Sin kasa ce da ke da al’ummar da yawansu ya kai biliyan 1.4 , daga cikinsu kuma yawan tsofaffi ya kai miliyan 267, kuma kasar tana ba da muhimmanci ga batun kare rayukansu da lafiyarsu. A cikin irin wannan yanayi, idan ba a dauki manufar “dakile cutar da zarar an gano ta ba” , lallai da wuya a yi zaton irin mummunan hali da kasar za ta samu kanta a ciki. Daga daukar matakin kulle a birnin Wuhan, zuwa daukar kwararan matakai na dakile cutar a sassan kasar da zarar an gano ta, ya sa kasar Sin ta yi ta samun nasarar dakile cutar, kuma hakan ya bayyana manufarta ta kare hakkin bil Adam.

Babu shakka, ana fuskantar hasarorin tattalin arziki bisa ga kwararan matakan da aka dauka na dakile cutar, amma kwalliya ta biya kudin sabulu, ganin yadda aka kai ga kare rayukan al’umma da ma al’ummarsu.

A sa’i daya kuma, yadda aka kai ga shawo kan cutar yadda ya kamata, ya kuma taimaka ga farfado da tattalin arziki. A shekarar 2020, a yayin da annobar ke addabar tattalin arzikin duniya, kasar Sin ce ta fara shawo kanta a duniya, haka kuma ta kasance a kan gaba a duniya wajen farfado da masana’antu da ma tattalin arziki. A shekarar 2021, tattalin arzikinta ya karu da kaso 8.1% bisa ma’aunin tattalin arzikin GDP.

Kwanan nan, mujallar New Scientist a wani bayanin da ta wallafa, ta bayyana cewa, “Kasashen da suka rungumi manufa da ka’idojin kawar da covid-19 baki daya, su ne mafiya samun nasara wajen yaki da cutar, daga rage mutuwar mutane, zuwa bunkasar tattalin arziki. Idan da a ce kasashe da dama sun amince da wannan dabara, da al’ummun duniya sun samu saukin cutar.”

Haka lamarin ya ke, manufar “dakile cutar da zarar an gano ta” ta taimaka ga kare rayuka da lafiyar al’umma mazauna kasar Sin. Baya ga haka, manufar ta kuma kiyaye karuwar tattalin arzikin kasar, wadda ta kuma samar da gudummawa wajen kiyaye tsarin masana’antun samar da kayayyaki a duniya da ma karuwar tattalin arzikin duniya. Ma iya cewa kasar Sin na daga cikin kasashen da suka fi samun nasarar yaki da cutar a fadin duniya, ko ta fannin yawan mutanen da suka harbu da cutar da yawan mutanen da cutar ta halaka, ko kuma ta fannin bunkasuwar tattalin arziki.

Idan kuma muka kalli kasashen da suka nuna halin “ko-in-kula” game da cutar, misali a kasar Burtaniya, wadda ta sanar da shirin “kasancewa tare da Covid-19” , inda bisa ga shirin aka daina killace wadanda suka harbu da cutar, kuma gwamnati ma ta daina gano wadanda suka yi cudanya da masu kamuwa da cutar. Amma bisa ga sabuwar kididdigar da kasar ta fitar, daga cikin ‘yan kasar 13, akwai daya da ya/ta harbu da cutar. Sakamakon binciken ya kuma nuna cewa, sakamakon yaduwar cutar nau’in Omicron BA.2, mutane ‘yan sama da shekaru 55 da suka harbu da cutar na karuwa cikin sauri tun daga watan Maris, wadanda suka ninka na baya har sau 20. Masana ma sun yi gargadin cewa, tsofaffi sun fi fuskantar hadarin mutuwa a sakamakon cutar. A kasar Amurka kuma, yaduwar cutar nau’in Omicron BA.2 ta haifar da karuwar masu harbuwa da cutar, kuma tuni yawan mutanen da cutar ta halaka a kasar ya wuce miliyan daya.

Yadda kasar Sin take da dimbin al’umma musamman tsofaffi, ya sa ba ta kawar da kai ga cutar ba, in ba haka ba, da wuya a yi zaton hasarorin rayuka da tattalin arziki da za a fuskanta a kasar. Kamar dai yadda mujallar New Scientist ta ce, “Ko yadda wasu kasashe suka yi watsi da manufar ‘dakile cutar Covid-19 da zarar an gano ta’ na nufin cewa manufar ba ta dace ba? Amsa ita ce lokaci ne kadai da ake ganin ceton rayukan al’umma da kiyaye karuwar tattalin arziki bai dace ba.” 

Rayuka da lafiya sune tushen hakkin dan Adam, idan babu su, to babu zancen hakkin dan Adam ta sauran fannoni. Akwai rashin tabbas ta fannin yanayin cutar da ake fuskanta, amma abu dake zama tabbas shi ne yadda kasar Sin ke kare rayukan al’ummarta da ma lafiyarsu.(Lubabatu)