logo

HAUSA

Sin ta aike da magunguna da kayayyakin lafiya ga Sudan ta kudu

2022-04-14 10:02:39 CMG Hausa

Kasar Sin ta aike da tawagar kiwon lafiya karo na tara zuwa kasar Sudan ta kudu dauke da gudunmawar magunguna da kayayyakin kiwon lafiya zuwa wani babban asibitin kasar.

Yolanda Awel, ministar lafiyar Sudan ta kudu, wadda ta karbi sabon rukunin kayayyakin kiwon lafiyar a Juba, babban birnin kasar Sudan ta kudu, ta yaba da kyakkyawar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

A lokacin bikin mika kayayyakin, Awel ta ce, ta yabawa kyakkyawar dangantakar dake tsakanin gwamnatocin Sudan ta kudu da Sin. Ta ce hadin gwiwar za ta ci gaba da kasancewa tsakanin kasashen biyu a fannonin kiwon lafiya daban-daban a nan gaba.

Ta kara da cewa, za su yi kyakkyawar amfani da kayayyakin lafiyar da magungunan yadda ya kamata.

Hua Ning, jakadan kasar Sin a Sudan ta kudu, ya taya tawagar jami’an kiwon lafiyar kasar Sin bisa sadaukar da kan da suka yi don yiwa al’ummar kasar Sudan ta kudu hidima.(Ahmad)