Tashar ruwan ciniki cikin ‘yanci ta Hainan ta shaida karuwar bude kofa ta kasar Sin ga kasashen waje
2022-04-14 10:57:26 CMG Hausa
“Ba za a rufe kofar da aka bude ba, maimakon haka za a kara budewa”, wannan shi ne babban alkawarin da kasar Sin ta dauka ga duniya. Ci gaban da aka samu na gina tashar ruwan ciniki cikin 'yanci ta Hainan a cikin shekaru hudu da suka gabata, ya zama wani misali na kudurin kasar Sin na cika alkawuran da ta dauka.
A ranar 12 ga watan Afrilu, shugaban kasar Sin Xi Jinping, wanda ke ziyarar aiki a lardin Hainan, ya ziyarci yankin raya tattalin arziki na Yangpu, don fahimtar yadda yankin ke samun bunkasuwa, inda aka gina tashar ciniki cikin 'yanci da ke da salon musamman na kasar Sin.
Tashar jiragen ruwa ta ciniki cikin 'yanci, ta nuna matsayi mafi girma game da bude kofa ga kasashen waje a yanzu haka. A ranar 13 ga watan Afrilu na shekarar 2018, aka soma aikin gina tashar ciniki cikin ‘yanci mai salon kasar Sin a Hainan.
A cikin shekaru hudu da suka gabata, yawan adadin kayayyakin da ake shigowa da su daga kasashen waje, bisa manufar "Kawar da haraji baki daya" na tashar ya zarce yuan biliyan 7, kuma matsakaicin karuwar yawan jarin waje da ake amfani da shi a duk shekara ya kai kashi 79.4%, kana an aiwatar da manufofi fiye da 150, game da tashar ciniki cikin 'yancin da dai sauransu.
Wadannan nasarorin da aka samu sun shaida yadda kasar Sin ta kuduri aniyar fadada bude kofa ga waje, da kokarin samun nasara tare da sauran kasashen duniya.
Lokacin da aka fi shan wahala, kamata ya yi mu kara bude kofa. A cikin shekaru hudun da suka gabata, duk da fuskantar kalubale da dama, ciki har da yaduwar COVID-19, da yaki da tsarin dunkulewar tattalin arzikin duniya da dai makamatansu, kasar Sin tana sa kaimi ga aikin gina tashar ciniki cikin 'yanci bisa shirin da ta tsara.
A ranar 1 ga watan Janairun bana, aka fara aiki da yarjejeniyar abokantaka kan tattalin arziki na yankin (RCEP), inda aka yi hasashen cewa, tun daga Hainan har zuwa kasar Sin baki daya, wani sabon zagaye na bude kofa ga kasashen waje zai bai wa duniya damar raba damammaki daga dukkan fannoni, kana da ba da kuzarin da ake bukata wajen farfadowar tattalin arzikin duniya. (Mai fassara: Bilkisu Xin)