logo

HAUSA

Ta Yaya Amurka Ta Sanya Hakkin Dan Adam Ya Zama Makami

2022-04-14 21:44:04 CMG Hausa

Ranar 12 ga watan Afrilu, rana ce ta bakin ciki ga Amurkawa. A wannan rana da safe, aka harbe wata mai juna biyu ‘yar shekaru 28 da haihuwa, da wani yaro mai shekaru 12 baya ga wasu mutane fiye da 20 da ba su ji ba ba su gani ba a tashar jirgin karkashin kasa ta Brooklin a birnin New York na kasar Amurka. Wannan na zuwa ne a lokaci da majalisar harkokin wajen kasar Amurka ta fitar da rahoton kasa da kasa na shekarar 2021 dangane da hakkin dan Adam, inda ta soki kasashe kusan 200 a duniya. Sai dai kamar ta saba, rahoton na Amurka bai ambaci yadda take kiyaye hakkin dan Adam a cikin gida ba.

Ta kau da kai daga harbe-harben da aka yi kan Amurkawa, inda ta mayar da hankali kan yadda ake kiyaye hakkin dan Adam a kasashen duniya. Abin da Amurka ta yi, ya nuna yadda take nuna munafunci kan kare hakkin dan Adam da danniya a duniya.

A shekarun baya, Amurka tana amfani da batun hakkin dan Adam a matsayin makami a sassa da dama na duniya, ciki hadda kasashen Iraki, Afghanistan, Syria, gabashin Turai da ma yankin Balkan, inda ta haifar da munanan matsalolin jin kai da dama. Sakamakon nazarin da kwalejin nazarin al’amuran kasa da kasa da na al’umma na Waston da ke jami’ar Brown ya gudanar a bara ya nuna cewa, yake-yaken da Amurka ta gudanar cikin shekaru kusan 20 da suka wuce da sunan wai yaki da ta’addanci sun sanya mutane fiye da dubu 929 rasa rayukansu.

Abin da aka yi ba’a shi ne bayan barkewar rikicin kasar Ukraine, Amurka wadda ta tayar da rikicin ta karbi ‘yan gudun hijira 12 kawai a watan Maris, a maimakon dubu 100 kamar yadda ta yi alkawari a baya.

Yadda Amurka ta nuna munafunci kan kiyaye hakkin dan Adam da kuma mayar da batun tamkar makami, ya fusata kasashen duniya. Jaridar The Times of India ta ruwaito a ranar 13 ga wata cewa, ba a ji dadin yadda Amurka take fuskantar matsaloli daban daban a cikin gida ba, amma ta nuna fuska biyu kan yadda ake kiyaye hakkin dan Adam a kasashen duniya. (Tasallah Yuan)