logo

HAUSA

Bai Kamata Manyan Kasashe Su Yi Kasa A Gwiwa Kan Batun Kare Muhalli Ba

2022-04-14 15:26:50 CMG Hausa

Yayin da kasashe masu raunin tattalin arziki a sassan duniya daban daban ke dandana radadin tasirin sauyin yanayi, wata matsalar dake tunkaro duniya ita ce yadda wasu manyan kasashe ke jan kafa wajen sauke nauyin dake kan su na ba da tallafin kare muhalli.

A wasu yankunan karkarar kasar Kenya ga misali, mutane na fuskantar mummunan yanayin fari. Wasu yankunan ma sun shafe shekaru 2 ba tare da samun ruwan sama ba, sakamakon haka tsirrai da dabbobi sun mutu kana al’ummu da yawansu ya kai miliyan 4 za su bukaci agajin abinci cikin watanni masu zuwa. Baya ga kasar Kenya, a nahiyar Asiya Bangladesh na kashe kudi har dala biliyan 2 a duk shekara, a ayyukan magance tasirin sauyin yanayi, yayin da kuma wasu tsibiran kasar ke fuskantar barazanar bacewa daga duniya baki daya.

Sassan kasa da kasa sun lura da wannan kalubale, kuma a shekarar 2010, MDD ta kafa asusun GCF mai samar da tallafi ga kasashe masu tasowa a ayyukan inganta yanayi, musamman dakile tasirin hayaki mai dumama yanayi.

To sai dai kuma a baya bayan nan, wannan asusu ya yi gargadin cewa, akwai yiwuwar dakatar da irin wadannan ayyuka a kasashe masu tasowa idan har manyan kasashe suka gaza samar da kudaden da suka alkawarta.

Masu rajin kare muhalli da dama sun zargi kasar Amurka, daya daga manyan kasashen dake tallafawa asusun GCF da gazawa, wajen sauke nauyin da ke wuyanta na samar da kason kudade.

A shekarar 2014, lokacin tsohuwar gwamnatin Barack Obama, gwamnatin Amurka ta alkawartawa GCF tallafin dala biliyan 3, amma har zuwa karshen wa’adin ta dala biliyan 1 kacal ta bayar. Shi kuwa magajin sa Donald Trump, ko taro bai baiwa asusun na GCF ba. A yanzu kuma, asusun na bin gwamnatin Joe Biden bashin tallafin dala biliyan 2.

A shekarar 2019, kasashe 13 mafi yawa daga nahiyar Turai, da Koriya ta kudu da New Zealand sun sha alwashin ninka tallafin da suke samarwa asusun na GCF domin cimma nasarar ayyukan shekarun 2020 zuwa 2023. Bisa jimilla, kungiyar EU ta samar da kudi har dala biliyan 9 ga asusun. Sai dai kuma cikin dala biliyan 17 da suka shiga asusun, kaso 6 bisa dari ne kacal ya fito daga Amurka, duk da kasancewarta kan gaba a duniya wajen fitar da hayaki mai dumama yanayi.

Ko shakka babu, Amurka ta gaza wajen sauya alkiblarta ga sassan makamashi marasa gurbata yanayi cikin shekaru 10 da suka gabata. A shekarar 2017 da 2018, ta tallafa da kudin kare muhallin kasa da wanda kasashen Faransa, da Jamus da Japan ko Birtaniya suka bayar, duk kuwa da cewa tattalin arzikinta ita kadai, ya zarce na wadannan kasashe idan an hade su baki daya.(Saminu Alhassan)