logo

HAUSA

Kwalara ta kashe mutane 31 a Najeriya

2022-04-14 09:32:28 CMG Hausa

A kalla mutane 31 ne suka rasu a cikin wannan shekarar sakamakon barkewar cutar kwalara a Najeriya, hukumar dakile cututtuka masu yaduwa ta kasar NCDC ta bayyana hakan.

Jessica Akinrogbe, babbar jami’ar sashen gaggawa na hukumar NCDC, ta bayyanawa manema labarai a Abuja cewa, an samu jimillar mutane 1,359 da suka kamu da cutar kwalara a kasar daga watan Janairu zuwa yanzu.

Kwalara cuta ce dake haddasa barkewar zawo da amai inda ruwan jikin majinyatan ke karewa, lamarin da ke haddasa mutuwar gaggawa.

Akinrogbe ta ce, kimanin jihohi 15 ne annobar ta shafa, ta ce hukumar NCDC ta riga ta aike da tawagar jami’an lafiya masu ayyukan gaggawa zuwa jihojin da lamarin ya shafa domin dakile yaduwar cutar.

Yayin da damina ke karatowa a kasar, akwai bukatar daukar karin matakai don kandagarkin yaduwar cutar.(Ahmad)