Bana ake cika shekaru 4 da gina tashar teku ta cinikayya marar shinge dake Hainan
2022-04-13 12:52:23 CMG Hausa
Bana ake cika shekaru 4 da gina tashar teku ta cinikayya marar shinge dake Hainan na kasar Sin. Yanzu haka, tashar na kara janyo jarin waje, al’amarin da ya kara taimakawa ga ci gaban tattalin arzikin wurin. Kana, bana, shekara ce mai matukar muhimmanci, inda hukumar kwastam za ta kara sa ido kan harkokin shige da fice na tsibirin Hainan, abun da ya sa ake gaggauta aikin gina tashar teku ta cinikayya marar shinge.
Kididdiga ta nuna cewa, tun shekaru hudu da suka gabata kawo yanzu, Hainan na kara janyo jarin waje. A watan Janairu da na Fabrairun bana, yawan jarin wajen da Hainan ta jawo ya karu da sama da kashi 50 bisa dari.
A farkon shekarar da muke ciki kuma, an riga an tabbatar da wasu muhimman ayyuka 64 a bangarori 11, wadanda suka shafi raya tashar teku ta cinikayya, da karbar haraji, da ayyukan rigakafin manyan hadarurruka, al’amarin da ya nuna cewa, an fara aikin shirye-shiryen shigar da hukumar kwastam don ta kara sa ido kan harkokin shige da fice na Hainan.
A nasa bangaren, mataimakin darektan ofishin kwamitin zurfafa gyare-gyare daga dukkan fannoni na lardin Hainan, Zhang Huawei ya bayyana cewa:
“Za mu yi kokari a wasu fannoni biyu, wato aiwatar da manufar raya tashar teku ta cinikayya marar shinge don ta kara taka rawa, da kuma kara yin kirkire-kirkire ga tsari. Sa’annan kuma za mu duba nagartattun ka’idojin cinikayya na kasa da kasa, don taimakawa hukumar kwastam ta kara sa ido kan duk fadin tsibirin, ta yadda za’a kyautata yanayin kasuwanci, da inganta kwarewar tashar teku ta fannin yin takara a duk duniya.” (Murtala Zhang)