logo

HAUSA

Najeriya: Yawan wadanda zazzabin Lassa ya hallaka sun karu zuwa 132

2022-04-13 10:49:01 CMG Hausa

Karamin minista a ma’aikatar lafiya a Najeriya Olorunnimbe Mamora ya ce, adadin al’ummar kasar da suka rasu sakamakon harbuwa da cutar zazzabin Lassa a sassan kasar daban daban ya karu zuwa mutum 132, tun bayan sake bullar cutar a farkon shekarar nan.

Mr. Mamora wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwar da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu kwafi a jiya Talata ya ce, gwamnati na daukar matakan rage bazuwar wannan cuta.

A cewar ministan, ya zuwa yanzu, an samu masu dauke da cutar 691, cikin jimillar mutane 3,746 da aka yi zaton sun harbu a sassan jahohin kasar 23. Kaza lika adadin wadanda cutar ta hallaka ya karu da kaso 19.1 bisa dari.

A farkon shekarar nan, cibiyar dakile cututtuka masu yaduwa ta kasar ko NCDC a takaice, ta ce ta fitar da dabarun hadin gwiwar sassa daban daban domin dakile bazuwar cutar Lassa a Najeriya.    (Saminu)