logo

HAUSA

Hannu Daya Ba Ya Daukar Jinka

2022-04-13 17:49:07 CMG Hausa

Alkaluma na tabbatar da cewa, sama da mutane miliyan shida ne suka mutu ya zuwa yanzu, tun bayan barkewar annobar COVID-19, yau shekaru biyu da suka gabata. Darasin da masana lafiya da jami’an kasa da kasa ke cewa, ya zama tilas a mayar da hankali a kai.

Sai dai yayin da wasu kasashen duniya, kamar kasar Sin suka yi nasarar aiwatar da managartan matakan dakile yaduwar annobar, baya ga taimaka kasashe da kungiyoyin kasa da kasa da kayayyakin yaki da cutar a lokuta daban-daban, a hannu guda kuma wasu kasashe irin su Amurka, na neman siyasantar da batun annobar, lamarin da ya haddasa hasarar rayukan mutane masu tarin yawa. Kuma har yanzu tula ba ta rabu da kalaye ba.

Hanya guda kamar yadda mahukuntan kasar Sin ke kira a koda yaushe wajen ganin an yaki wannan annoba da ma kalubalolin dake addabar duniya, ita ce cudanyar sassan kasa da kasa.

Sanin kowa ne cewa, abu mafi muhimmanci shi ne mayar da jama’a da ma al’umma baki daya a gaban komai. Kuma shi ne matakin da zai daidaita alkiblarmu a dukkan fannoni. Yanzu dai duniya na bukatar cudanyar dukkan bangarori fiye da kowane lokaci.

Buga da kari, bayan wucewar annobar COVID-19, ya zama tilas kasashen duniya su karfafa hadin gwiwa, karkashin laimar MDD, su martaba juna, da amincewa da juna da gaskata juna, su nuna fata na gari, da hadin gwiwa don cimma moriya tare, su kuma yi aiki tare don amfanin gaba. Saboda tuwon gobe ake wanke tukunya. Kuma malam Bahaushe na cewa, Hannu daya ba ya daukar jinka. (Ibrahim Yaya)