logo

HAUSA

Kamfanin kasar Sin ya kammala gina cibiyar koyar da sana’o’i a Ghana

2022-04-13 11:04:02 CMG Hausa

Kamfanin AVIC International Holding Corporation na kasar Sin, ya kammala ginin wata cibiyar koyar da sana’o’i a birnin Kumasi na kasar Ghana. Mahukuntan kamfanin sun ce cibiyar za ta bunkasa damar koyar da sana’o’i a kasar dake yammacin Afirka.

An fara aikin ginin ne a watan Nuwambar shekarar 2019, ta kuma kunshi sabon babban zauren gudanar da jarabawa na ma’aikatar ilimin kasar ta Ghana, da kuma cibiyar koyar da fannonin sana’o’i 15.

Kari kan hakan, kamfanin ya kuma samar da na’urorin koyar da sana’o’i 69 ga sassan cibiyar 23, wadanda za a yi amfani da su wajen horas da rukunonin malamai da dalibai, musamman a bangaren sarrafa injuna, da ayyukan lantarki, da walda, da gyaran na’urori, da fannin gine-gine.

Yayin kaddamar da cibiyar a birnin na Kumasi, ministan ma’aikatar ilimin Ghana Yaw Osei Adutwum, ya gabatar da sakon shugaba Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, tare da bayyana ilimin koyar da sana’o’i a matsayin jigon zamanantar da ayyukan masana’antun kasar, matakin da kuma zai samar da karin guraben ayyukan yi ga al’ummar Ghana.     (Saminu)