logo

HAUSA

Luo Haixiang dake mai da hankali kan kare lafiyar mazauna kauyan da ke cikin tsaunuka a cikin sama da shekaru 20

2022-04-12 17:35:32 CMG Hausa

Bayan Luo Haixiang ta sami takardar shaidar kammala karatun lokitanci, inda ta koma kauyensu don zama likita a cibiyar kiwon lafiya ta gundumarsu. Tun daga lokacin kuma, ta soma daukar nauyin taimakawa mazauna wurin wajen koya musu "sabuwar hanyar haihuwa", wato yadda likitoci ke taimaka wa mata masu juna biyu wajen haihuwa. A ganinta, aikin ba shi da wata wahala. Amma, ko shakka babu, ta raina wahalar da za ta iya gamuwa da ita.

Lokacin da ta je kauyen don koyawa mutane wannan sabuwar hanya, idanun Luo Haixiang ko da yaushe suna kan cikin matan. Duk wanda ya auri amarya, bayan wata biyu, za ta je gidansu don ta gaida su.

Ba wadda ke son fada mata cewa, ta samu ciki, har ma wasu matan dake nuna alamun sun samu ciki, su kan gudu yayin da suka ganta. Amma duk da haka, Luo Haixiang ta kan tambaye su, “Ko kin samu ciki? Ko kin je an duba lafiyarki?” Da jin haka, sai mazauna kauyen da suke yi mata kirki a yau da kullum, suka fara canza mata fuska, “Ke yarinya ce, me ya sa kike fadan maganganu na rashin kunya!”

Lokacin da ta sadu da wata mace da ta yarda a duba lafiyarta, sai Luo Haixiang ta yi kokarin ba ta shawarar zama ungozomarta. Amma, da jin haka, sai matar da danginta suka tura ta waje, suka kuma ce, “Wacce mace ce ba ta iya haihuwa a gida har ma ta yanke cibi da kanta? Ta yaya zan bukaci taimakonki?”

Wannan ba shi ne karon farko da Luo Haixiang ta taba jin irin wadannan kalamai ba. Wata rana, bayan da ta ziyarci wata mata mai juna biyu don duba lafiyarta bayan ta haihu, ta ji an ce, “Akwai abubuwan mamaki a duniyar nan, har akwai wadda ke son ganin wuraren da bai kamata a gani ba?”

Luo Haixiang ba za ta iya tuna sau nawa, ta buya a gida tana kuka ba. A duk lokacin da ranta ya baci, sai ta rika tunanin cewa, “Me ya sa nake wannan aikin? Ba zan samu abin da zan ci ba ne idan ban yi aikin ba?” Amma, nan da nan sai ta share hawayenta, ta fada wa kanta cewa, “Ai zan iya barin aikin, amma idan na yi haka, matan kauyenmu za su ci gaba da zama cin wahala a lokacin haihuwa. Idan har na yi tsayin daka kan aiki na, ko da dan canji aka samu, zai taimakawa matan matuka.”

Kyauta maganin kiyayya, kuma alheri danko ne, ba ya faduwa kasa banza. Sakamakon kokarin da Luo Haixiang ta yi, tsarin gargajiyar da ake bi na daruruwan shekaru ya fara canzawa sannu a hankali, kuma mazauna kauye masu zurfin tunani, sun fara amincewa da aikinta a hankali.

Lokacin da ta tafi kauyen don ba da jinya, mata masu juna biyu sun fara kebewa da Luo Haixiang a wani wuri don yi mata tambaya, “Ba na jin dadi kwanan nan, don Allah ki taimake ni.” Bayan ta yi musu bincike, da kuma gaya musu abubuwan da ya kamata su lura da su, akwai wasu mata da kan kara da cewa, “Iyalina ba su a san kina taimaka min, don haka kar ki gaya wa kowa.” Idan ta ji haka, cikin murmushi, sai Luo Haixiang ta ce to. Aganinta, irin dan canjin da aka samu, ya isa ya karfafa mata gwiwa da ma jin dadi kwarai. Baya ga haka, akwai wadanda ke son ta taimaka musu a lokacin da su ka zo haihuwa.

Gao Tinghua tana zaune ne a garin Yunwu, mai tazarar kilomita goma sha biyu daga kauyen Baigu, tana kuma daya daga cikin mata kalilan a kauyen da ba su “jin tsoron” neman taimakon Luo Haixiang wajen haihuwa a shekarun 1980.

Gao Tinghua ‘yar uwar mijin wancan matar da ta mutu ne a lokacin haihuwa. A lokacin, ta riga ta haifi ’ya’ya biyu, kuma duk haifi da kanta ta haihu a lokacin sanyi, kuma ta yanke cibiya da simintin tangaran. Ba ta jin tsoron a lokacin. Amma, mutuwar matar wanta ta tsorata Gao Tinghua sosai. Saboda haka, yayin da take da juna biyu ta ’ya mace, ta dage kan likita Luo Haixiang ne za ta karbi haihuwar. Amma, ra’ayin ta ya gamu da adawa daga wajen mijinta da surukinta wato mahaifin mijinta, duk da haka, Gao Tinghua ta dage kan cewa, “Rayuwata tawa ce, dole ne likita ta karbi haihuwa ta.”

Gao Tinghua ta tuna cewa, a ranar da za ta haihu, shekarun likita Luo Haixiang 18 ne kawai a lokacin, ta koya mata yadda za ta rika yin nishi wajen haihuwa, ta kuma taimaka mata yanke cibiya, da tsaftace abin da haifa. Gao Tinghua ta ce, “Likita Luo ta kwantar min hankali. Kuma wannan shi ne karo na farko da ban bukaci komai ba, a yayin haihuwa, sai dai na kwanta in huta bayan na haihu.”

“Haifuwa bisa taimakon likita, ya fi tsaro da kwanciyar hankali”, wannan sako ya fara bazuwa sannu a hankali a tsakanin ’yan matan dake kauyen. Luo Haixiang ta tuna cewa, tun daga farkon shekarun 1990, mata masu juna biyu da yawa suna son ta duba lafiyarsu ta kuma taimaka musu a wajen haihuwa. Wannan ya karfafa mata gwiwa kan ayyukanta.

Sannu a hankali, aka daina samun mace-macen mata masu juna biyu da jarirai a kauyen. Mata suna zuwa awu asibiti a kan lokaci domin a duba lafiyarsu da zarar sun samu ciki. “Duk mai tambaya, tana iya bugawa likita Luo waya a kowane lokaci”, “Ana kuma yiwa jarirai alluran rigakafi daban-daban a kan lokaci kamar yadda likita Luo ta jaddada bayan da matan suka sauka lafiya”, wadannan shi ne yanayin da matanen kauyen suke a halin yanzu.

Yanzu, matan da ke kauyen suna daukar Luo Haixiang a matsayin danginsu, su kan ce, “Likita Luo ta fada mana cewa, rayuwar mace ita ce rayuwa, kuma dole ne mu kyautata makomarmu da kan mu!”

A kasar Sin, akwai likitoci sama da 740,000 dake aiki a kauyuka kamar Luo Haixiang, kuma ba wai kawai suna kare lafiyar mazauna yankunansu ba, har ma suna inganta rayuwar mazauna kauyukan a fannin kiwon lafiya, da kuma kokarin inganta samun ci gaba ta wannan fuska.