logo

HAUSA

Mataimakin shugaban Najeriya zai yi takarar shugabancin kasar a 2023

2022-04-12 10:07:28 CMG Hausa

Mataimakin shugaban kasar Najeriya Yemi Osinbajo, a ranar Litinin ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar neman shugabancin Najeriya a babban zaben kasar mafi yawan al’umma a nahiyar Afrika a shekara mai zuwa.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na twita, Osinbajo ya ce, yana fatan tsayawa takarar a karkashin jam’iyyar APC mai mulki.

Osinbajo ya ce, damar da ya samu na yiwa kasar hidima na tsawon shekaru bakwai a matsayin mataimakin shugaban kasa ga jajurtaccen dan kishin kasa, mai bautawa kasa da tabbatar zaman lafiya, da kare ’yancin kasa, kuma mutum mai nagarta shugaba Muhammadu Buhari.

Osinbajo, farfesa a fannin shari’a, an zabe shi tare da shugaba Buhari a shekarar 2015 domin tafiyar da al’amurran kasar ta yammacin Afrika. An kuma sake zabarsu a shekarar 2019 a karo na biyu a karkashin jam’iyyar APC mai mulkin kasar. (Ahmad)