logo

HAUSA

Ya Zama Tilas Japan Ta Dakatar Da Shirin Zubar Da Ruwan Dagwalon Nukiliya Cikin Teku

2022-04-12 21:15:37 CMG Hausa

Ranar 13 ga watan Afrilun shekarar 2021, gwamnatin kasar Japan ta sanar da kudurin zubar da ruwan dagwalon nukiliya daga tashar samar da wutar lantarki ta makamashin nukiliya dake Fukushima a cikin teku. Kwanan baya, kamfanin wutar lantarki na Tokyo ya kau da kai daga zargin da kasashen duniya ke yi kan wannan batu da kuma kin yarda daga al’ummar Japan fiye da dubu 180, inda ya shirya gina wurin da za a zubar da ruwan dagwalon nukiliyar a karkashin ruwan teku a kwanaki 10 na tsakiyar watan Afrilun bana. Kafofin yada labaru na Japan sun ruwaito cewa, kamfanin ya kammala ayyuka a doron kasa, tare da gudanar da sauran ayyuka. An kiyasta cewa, za a zubar da ruwan dagwalon nukiliyar a hukumance a lokacin bazara na shekarar 2023.

Zubar da ruwan dagwalon nukiliyar cikin teku ya shafi Japan da ma tsaron yanayin muhalli na duniya baki daya da kuma lafiyar al’ummar kasa da kasa. Yanzu an adana fiye da tan miliyan 1 da dubu 250 na ruwan dagwalon nukiliyar a tashar samar da wutar lantarki bisa makamashin nukiliya ta farko dake Fukushima. Ko da yake Japan ta yi shelar cewa, za a tsabtace ruwan kafin a zuba shi a cikin teku. Amma masu nazari sun yi nuni da cewa, kila sinadarin nukiliya dake cikin ruwan zai iya shiga jikin dabbobin dake rayuwa a cikin teku, kana daga bisani su shiga jikin dan Adam. Sun kuma yi kiyasta cewa, sinadarai masu guba za su iya mamaye sama da rabin tekun Pasifik cikin kwanaki 57 bayan zuba ruwan cikin teku, kuma hakan na iya gurbata tekunan kasa da kasa baki daya bayan shekaru 10.

Yarjejeniyar MDD da ta shafi kiyaye teku ta dora wa kasa da kasa alhakin kiyaye muhallin teku. Don haka, wajibi ne su sauke nauyin dake bisa wuyansu bisa dokokin kasa da kasa. Idan Japan ta ci gaba da shirinta, to, kasashen Asiya da na yankin tekun Pasifik dake makwabtaka da ita suna da ikon daukar matakai, za kuma su nemi diyya daga wajen Japan ta hanyar kai ta kara a hukumomin aiwatar da doka na kasa da kasa. (Tasallah Yuan)