logo

HAUSA

Yan bindiga sun hallaka wani kusa a jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya

2022-04-12 09:52:37 CMG Hausa

Rahotanni daga rundunar ‘yan sandan Najeriya na cewa, wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba, sun harbe Mr. Gbenga Ogbara, kusa a jam’iyyar APC mai mulki reshen jihar Osun, dake kudu maso yammacin kasar.

Da take tabbatar da hakan cikin wata sanarwa, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar ta Osun Yemisi Opalola, ta ce bayan kisan Mr. Ogbara da sanyin safiyar jiya Litinin a gidansa dake garin Igangan, ‘yan sanda sun bazama domin farauto wadanda suka aikata wannan ta’asa.

Opalola ta kara da cewa, an garzaya da gawar mamacin asibiti, kuma ‘yan sanda na ci gaba da bincike game da dalilin aukuwar kisan gillar. Daga nan sai ta alkawarta cafke wadanda suka hallaka dan siyasar, tare da gurfanar da su gaban kuliya. (Saminu)