logo

HAUSA

Kamfanin Sin ya samar wa daliban firamaren Habasha dake fama da talauci wasu kayayyakin karatu

2022-04-11 13:26:26 CMG Hausa

 

A ranar 9 ga wata, reshen kamfanin CCECC na kasar Sin dake kasar Habasha, ya samar wa daliban firamaren kasar masu fama da talauci 100 dake birnin Addis Ababa, fadar mulkin kasar wasu kayayyakin karatu.

Rahotannin sun bayyana cewa, kayayyakin karatun da kamfanin kasar Sin ya samar sun hada biro da litattafai, da jakar adana litattafai da sauransu, kana kamfanin ya samar wa daliban wasu kayayyakin wasan motsa jiki ciki har da teburin wasan kwallon tebur, da kwallon tebur.

Mataimakin shugaban hukumar ba da ilmi ta birnin Addis Ababa Ademasu Dechasa, ya bayyana yayin bikin mika kayayyakin cewa, gwamnatin kasar Sin da jama’ar kasar, sun samar da goyon baya matuka ga ci gaban kasarsa ta Habasha, musamman ma wajen ba da ilmi, ya kuma nuna fatan cewa, kasar Sin za ta ci gaba da samar da tallafin a fannin.

A nasa bangaren kuma, babban manajan kamfanin CCECC na kasar Sin reshen kasar Habasha Zheng Chongfeng ya bayyana cewa, aikin ba da ilmi yana da muhimmanci kwarai ga ci gaban kasa, kuma kamfaninsa yana samar da tallafi wajen ba da ilmi ga Habasha ne, bisa shawarar ziri daya da hanya daya. (Jamila)