Huldar Sin da Najeriya: Ko haka tana cimma ruwa?
2022-04-11 19:04:24 CMG Hausa
Tun bayan shafe fiye da shekaru 50 da kulla huldar diflomasiyya a tsakanin kasashen Sin da Najeriya, har yanzu, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu tana kara inganta da kuma fadada zuwa dukkan fannoni. To shin ko haka tana cimma ruwa a huldar dake tsakanin bangarorin biyu? Hakika, duba da girman tasirin huldodin dake tsakanin kasashen biyu, za mu iya cewa, an cimma manyan nasarori cikin wadanan gomman shekaru da suka gabata. Idan za mu iya tunawa, a ranar 10 ga watan Fabrairun shekarar 1971 ne aka kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashen Sin da Najeriya, wato sama da shekaru 51 ke nan da suka gabata. Duba da yanayin muhimmancin huldar dake tsakaninsu, jami’ai da mahukunta bangarorin biyu suna ci gaba da kulla yarjejeniyoyin kasuwanci gami da shirya tarukan karawa juna sani da musaya a fannonin bunkasa ilmi, da kiwon lafiya, da yaki da annobar COVID-19 a tsakanin kasashen biyu da nufin kyautata huldar dake tsakaninsu. Alal misali, a baya bayan nan, an gudanar da taron kwamitin hadin gwiwa tsakanin Sin da Nijeriya karo na bakwai, game da batun harkokin tattalin arziki, da cinikayya, da fasahohi. Kwamitin ya gudanar da taron ne ta kafar bidiyo karkashin jagorancin mataimakin ministan cinikayya na kasar Sin Qian Keming, da ministar kudi da tsare-tsaren tattalin arziki ta Najeriya, Zainab Ahmed. Jakadan kasar Sin Cui Jianchun, da mambobin kwamitin daga kasashen biyu ne suka halarci taron ta kafar intanet. Kasashen biyu sun waiwayi kyawawan nasarori da suka cimma a hadin gwiwarsu da ya shafi ciniki, da zuba jari, da ababen more rayuwa, inda kuma suka yi musayar ra’ayoyi game da kara inganta hadin gwiwarsu ta fannin tattalin arziki da ciniki. Haka kuma, bangarorin biyu sun sake jaddada aniyarsu ta kara zurfafa hadin gwiwarsu, musamman ta fannin manyan ayyuka 9 da aka cimma yayin taron ministoci karo na 8 na dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika, da kuma muhimman bangarori 9 na Nijeriya, tare da ci gaba da kyautata walwalar jama’ar kasashen biyu, da raya dangantakarsu ta fuskar tattalin arziki da ciniki cikin aminci. Ko shakka babu, idan aka yi la’akari da bunkasuwar huldar dake tsakanin bangarorin biyu ta fannonin ciniki da tattalin arziki, da cudanyar al’adu, da hulda tsakanin mutum da mutum na kasashen biyu, za mu iya cewa, haka tana cimma ruwa, kuma kwalliya tana biyan kudin sabulu. (Ahmad Fagam)