logo

HAUSA

Ba zai yiwu NATO ta cimma burinta na tayar da tarzoma ba

2022-04-11 14:29:16 CMG Hausa

Kwanan baya kungiyar NATO ta kira taron ministocin harkokin waje a hedkwatarta dake birnin Brussels na kasar Belgium, inda aka gayyaci ministocin harkokin wajen kasashen Japan, da Koriya da Kudu, da Australia, da New Zealand, dake yankin Asiya da tekun Pasifik, domin su halarci taron.

Yayin taron, mahalartan sun tattauna na tsawon lokaci kan kasar Sin, kuma sun soki matsayin da kasar Sin ta dauka kan batun Ukraine ba gaira ba dalili. Kaza lika babban sakataren kungiyar Jens Stoltenberg, ya yi tsokaci da cewa, ya dace a yi la’akari kan yadda ake yaki da kasar Sin, yayin da ake tsara sabon shirin raya kungiyar.

Yanzu haka rikici yana ci gaba da barkewa a Ukraine, kuma kungiyar NATO wadda ke da manufar yakin cacar baka, tana son tayar da tarzoma a yankin Asiya da tekun Pasifik, lamarin da ya nuna mummunan yunkurin kungiyar bisa matsayinta na kayan nuna fin karfi na kasar Amurka, amma ba zai yiwu ta cimma burinta ba, saboda matakan da ta dauka sun sabawa tafiya da zamani. (Jamila)