Babbar matsin lambar da masu ciki ke fuskanta za ta kara wa ‘ya’yansu barazanar kamuwa da cutar dake addabar mutum cikin dogon lokaci
2022-04-10 14:56:43 CMG Hausa
Masu nazari daga kasar Australiya sun gano cewa, idan masu juna biyu ba su da koshin lafiya a jiki da ma tunani, to, ‘ya’yansu za su kara fuskantar barazanar kamuwa da cututtukan da ke addabar mutum cikin dogon lokaci, yayin da suke matsayin jarirai da kuma matasa.
Masu nazari daga jami’ar Southern Queensland ta kasar Australiya sun tantance halin da kananan yara fiye da dubu 5 da kuma mahaifansu mata suke ciki a jiki da ma tunani. Sakamakon tantancewar ya nuna cewa, akwai wata alaka a tsakanin halin da mahaifa mata suke ciki a jiki da tunani yayin da suke samun ciki da kuma shekara guda bayan haihuwa, da kuma lafiyar ‘ya’yansu. Idan masu juna biyun sun kamu da ciwon hawan jini, ciwon zuciya, ciwon sukari da sauran cututtukan da ke addabar mutum cikin dogon lokaci, to, ‘ya’yansu za su kara fuskantar babbar barazanar kamuwa da irin wadannan cututtuka yayin da suke matsayin jarirai da kuma matasa. Sa’an nan kuma, idan mahaifan mata sun yi fama da bakin ciki ko damuwa yayin da suke samun ciki da kuma shekara guda bayan haihuwa, to, jariransu za su kara samun yiwuwar kamuwa da ciwon asma, ciwon borin jini da sauran cututtukan da ke addabar mutum cikin dogon lokaci.
Har ila yau, idan masu juna biyun sun sha giya fiye da sau daya a kowane mako, to, ‘ya’yansu sun fi yiwuwar gamuwa da matsalar lafiya har sau 1 da wani abu. Haka kuma, idan masu juna biyun ba su ci kwai, kifi ba, kuma ba su sha madara ba, ko kuma tsawon lokacin da suka dauka wajen shayar da jariransu nonon uwa zalla bai kai watanni 6 ba, to, jariransu su kan gamu da mummunar matsalar lafiya. Amma idan masu juna biyun sun motsa jiki, to, ‘ya’yansu su kan kasance cikin koshin lafiya.
Madam Zhang Chuji, wata likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi mana karin bayani da cewa, halin da masu juna biyu suke ciki a jiki da ma tunani da kuma magungunan da suka sha, su kan haifar da illa ga ‘yan tayinsu. Alal misali, ko sun yi fama da ciwon asma, ciwon sukari, ciwon hawan jini ko a’a? Ko sun sha maganin ciwon bakin ciki da cututtukan borin jini da maganin kau da kwayoyin cuta ko a’a? Nazarin ya jaddada muhimmancin lafiyar masu juna biyu a jiki da ma tunani. (Tasallah Yuan)