Ado Ahmad Gidan Dabino: Ina kira ga Hausawa su rike harshe da al’adunsu kamar yadda Sinawa suke yi
2022-04-09 20:33:27 CMG Hausa
Ado Ahmad Gidan Dabino, MON, shahararren marubuci gami da mawallafin littattafai ne, kuma jarumin fina finai, kana fitaccen mai shirya fina-finan a arewacin Najeriya.
A zantawarsa kwanan nan tare da Murtala Zhang, Alhaji Ado Ahmad Gidan Dabino ya yabawa wasu mutanen kasar Sin sosai, saboda jajircewarsu wajen karatu da yayata harshe da al’adun Hausa, inda kuma ya bayyana wasu hanyoyin da za’a iya bi wajen raya harshen Hausa bisa hadin-gwiwar kasar Sin da tarayyar Najeriya.
A karshe, Ado Ahmad Gidan Dabino, MON, ya yi kira ga al’ummar Hausawa da su rike harshe da al’adunsu kamar yadda mutanen kasar Sin suke yi. (Murtala Zhang)