logo

HAUSA

An gudanar da taron kwamitin hadin gwiwa tsakanin Sin da Nijeriya

2022-04-09 17:08:53 CMG Hausa

An gudanar da taro karo na 7 na kwamitin hadin gwiwa tsakanin Sin da Nijeriya, kan harkokin tattalin arziki da cinikayya da fasahohi, a jiya Juma’a.

Kwamitin ya gudanar da taron ne ta kafar bidiyo karkashin jagorancin mataimakin ministan cinikayya na kasar Sin Qian Keming da ministar kudi da tsare-tsare ta Nijeriya, Zainab Ahmed. Jakadan kasar Sin Cui Jianchun da mambobin kwamitin daga kasashen biyu ne suka halarci taron ta kafar intanet.

Kasashen biyu sun waiwayi kyawawan nasarori da suka cimma a hadin gwiwarsu da ya shafi ciniki da zuba jari da ababen more rayuwa, inda kuma suka yi musayar ra’ayi a kan kara inganta hadin gwiwarsu ta fannin tattalin arziki da ciniki.

Haka kuma, a shirye bangarorin biyu suke su zurfafa hadin gwiwarsu, musamman ta fannin manyan ayyuka 9 da aka cimma yayin taron ministoci karo na 8 na dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika da kuma muhimman bangarori 9 na Nijeriya, tare da ci gaba da kyautata walwalar jama’ar kasashen biyu da raya dangantakarsu ta tattalin arziki da ciniki cikin aminci. (Fa’iza Mustapha)