logo

HAUSA

Amurka na sharbar romon yaki yadda take so

2022-04-08 21:34:27 CMG Hausa

A ‘yan kwanakin baya, Amurka ta fitar da kasafin kudin ta na shekarar 2023, mai kunshe da bukatar bunkasa kasafin ayyukan soji. Da ma dai kaso mai tsoka na kasafin kudin Amurka na fannin ayyukan soji, suna tafiya ne a ayyukan soji da take gudanarwa a ketare.

Bayan yakin duniya na II, Amurka ta shiga yakin Korea, da na Vietnam, da na yankin Gulf, da na Afghanistan da Iraqi. Ana ma iya cewa cikin kusan karni 2 da rabi tun bayan kafuwar kasar, shekaru 20 ne kadai kasar ta Amurka ba ta cikin yaki. Amurka ta kan shiga yaki kai tsaye, tana taimakawa masu aiwatar da yakin, tana kuma ingiza masu adawa da gwamnatoci su yi fito na fito da mahukunta, ta hanyar samar masu da makamai da harsasai. A wasu lokutan kuma, tana horas da dakaru masu yakar gwamnatin kasashe, don haka a iya cewa, Amurka ta kafa tarihin tsoma hannu cikin al’amuran kasashe masu tarin yawa. Tun daga karshen yakin duniya na II a shekarar 1945 zuwa 2001. Cikin tashe tashen hankula 248 da suka wakana a yankunan duniya 153, Amurka ce ta rura wutar 201 daga cikin su.

Abun tambaya shi ne, me ya sa Amurka ke matukar son yaki? Amsa ita ce, baya ga burin ta na yin babakere a duniya, tana kuma neman cimma muradun manyan kamfanonin sarrafa makamai nata, wadanda rundunar sojin kasar, da dillalan makamai, da ‘yan siyasar kasar ke goyawa baya.

Idan har babu yaki, dole ne Amurka ta bullo da wani, domin wanzar da ribar da wadannan manyan kamfanonin makamai ke kwadayi, yayin da sauran sassa masu cin riba daga yakin ke jiran nasu kason. (Mai zane: Mustapha Bulama)