Tunawa da wani farfesa da ya yi kokarin bautawa jama’a
2022-04-08 14:24:49 CMG Hausa
A ranar 5 ga watan Afrilu, jama’ar kasar Sin sun yi bikin Qingming na gargajiya, wanda ya kasance wani biki, kuma rana ce ta musamman da aka kebe, domin tunawa da mambobin iyali da suka riga suka rasu. Don zama dacewa da al’adar wannan biki na musamman, a yau ma a cikin shirinmu za mu tuna da wani tsohon farfesa mai kirki, mai suna Li Baoguo, wanda ya yi kokarin bautawa jama’a, har ma ya sadaukar da ransa a karshe.