logo

HAUSA

Ruhun wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing yana kara daraja a yayin da ake cike da tashin hankali

2022-04-08 21:09:33 CMG Hausa

Yau Jumma’a, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da muhimmin jawabi a gun taron nuna yabo ga wadanda suka taka rawar gani yayin wasannin Olympics na lokacin sanyi da na nakasassu na lokacin sanyi na birnin Beijing, inda ya bayyana cewa, kasar Sin ta cika alkawarin da ta dauka ga al'ummomin kasa da kasa, ta gudanar da gasar wasannin Olympics mai sauki, tsaro da ban mamaki.

Lokacin da ake gudanar da wasannin Olympics na lokacin sanyi da na nakasassu na lokacin sanyi na Beijing, yanayin annobar da duniya ke ciki yana da sarkakiya da tsanani. Don haka, duk duniya na mayar da hankali kan ko matakan rigakafin annobar COVID-19 na kasar Sin, za su iya jure jarrabawar ko a’a. A karshe kasar Sin ta mika takardar amsa dake cewa, ta ba da fasahohi masu amfani ga yaki da cutar a duniya, da kuma gudanar da manyan bukukuwan kasa da kasa.

Ta hanyar shirya wasannin Olympics na lokacin sanyi da na nakasassu na lokacin sanyi na Beijing, duniya ta ga wata kasar Sin mai bude kofa ga kasashen waje, wadda ke neman daukaka.

Shugaban kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa Thomas Bach, ya kira gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing “Gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi mara misaltuwa".

Abun da ya cancanci a lura a nan shi ne, nasarar da aka cimma ta gudanar da wasannin Olympics na nakasassu na lokacin sanyi a nan birnin Beijing, ya kuma zama wata taga da za ta baje kolin ra'ayoyin kasar kan kare hakkin dan Adam, da nasarorin da ta samu a wannan fanni. Kamar yadda shugaba Xi ya ambata a cikin jawabinsa, game da kalmar wani dan wasan kasar Sin mai fama da matsalar gani, wato "Ba na iya ganin duniya, amma ina son duniya ta gan ni", wadda ke nuni da irin nasarorin da kasar Sin ta samu, wajen mutuntawa da kare hakkin nakasassu.

Abu mafi muhimmanci a nan shi ne, a cikin duniya mai cike da tashin hankali, ruhin wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing ya cancanci a yi koyi da juna cikin sa tsakanin al'ummomin duniya, da shuka tsabar hadin kai da ta abota, da kuma inganta damar jama’ar kasashe daban daban su “hadu domin amfanin gaba.” (Mai fassara: Bilkisu Xin)