logo

HAUSA

Ayyukan soji a Nijeriya sun yi sanadin mutuwar gomman ‘yan ta’adda

2022-04-08 10:14:02 CMG Hausa

 Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta ce, ayyukan sojojinta sun yi sanadin kashe gomman ‘yan ta’adda a yankin arewa maso gabashin kasar cikin makonni biyu da suka gabata.

Kakakin rundunar Bernard Onyeuko, ya bayyanawa manema labarai jiya a Abuja babban birnin kasar cewa, yayin ayyukan sojin da aka gudanar daga ranar 25 ga watan Maris zuwa jiya Alhamis, an kama akalla ‘yan ta’addan da suka hada da masu leken asiri 22, da mayaka 11, da masu samar musu da kayayyaki 3.

Har ila yau, kakakin ya ce, an kuma ceto wasu fararen hula 30 da kungiyar BH da ta ISWAP suka yi garkuwa da su. (Fa’iza Mustapha)