logo

HAUSA

Sin ta zama zakaran gwajin dafi a fannin tallafawa sassan kasa da kasa

2022-04-07 20:27:25 CMG Hausa

A duniyar yau mai cike da sauye sauye, kasashen duniya na ci gaba da kyautata hadin gwiwa, tare da fadada manufofin su na cudanya da kasashen waje. Bisa shaidu na zahiri, muna iya cewa kasar Sin na cikin kasashe kalilan dake samun karin martaba a fannin sauke nauyin dake wuyan ta, game da tallafawa sauran kasashen duniya, karkashin managartan manufofin ta na waje, da sauye sauye da take gudanarwa daidai da zamani.

Kasar Sin ta zama wani misali, na irin burin da ake da shi game da tallafawa kasashe musamman masu tasowa, domin kawar da kalubalen bai daya dake addabar duniya, da kuma hade sassan tattalin arziki domin moriyar kowa da kowa.

Ko shakka babu, cikin shekarun baya bayan nan, babbar manufar nan ta gina al’ummar duniya mai makomar bai daya, da fadada tattaunawa, da cin moriyar juna tsakanin sassan al’ummun duniya, ta samu gagarumar nasara, inda manufar ke agazawa ci gaban duniya, da taimakawa kasashe masu rauni.

Karkashin manufofin hangen nesa na shugaban kasar Sin Xi Jinping, da jagorancin jam’iyyar Kwaminis mai mulkin kasar, na gudanar da ayyukan da suka kamata bisa tsari, da sauye sauye a fannonin raya tattalin arziki, da kyakkyawan salon siyasa, Sin ta samar da wani dandali na hade sassa daban daban, ta kuma fadada tallafin ta ga sauran kasashe mabukata, ta dukkanin hanyoyi gwargwadon ikon ta.

Tallafin jin kai da Sin ke samarwa kasashe, ya haifar da babban tasiri a shekarun baya bayan nan, inda Sin din ke hada ayyukan jin kai da hadin gwiwar samun bunkasuwa tare. Karkashin hakan, Sin ta tallafawa kasashe sama da 50 da alluran rigakafin cutar COVID-19, aikin da ya yi matukar samun yabo da jinjinawa daga al’ummun duniya.

Kaza lika, Sin ta yi rawar gani wajen ba da agajin kawar da manyan kalubale da duniya ke fuskanta, kamar fannin sauyin yanayi, da hada hadar cinikayya, da raya tattalin arziki, da kara kyautata harkokin diflomasiyyar kasa da kasa.

A ‘yan kwanakin baya ma, Sin ta gudanar da jerin tarukan kasa da kasa, tare da abokan huldar ta na shiyyar da take a birnin Tunxi, na lardin Anhui, inda sassan suka tattauna batutuwa da suka jibanci raya tattalin arziki, da samar da tallafin jin kai ga makwafciyar ta Afghanistan. (Saminu Alhassan)