logo

HAUSA

Jami’in MDD ya yi maraba da kafa tawagar wucin-gadi ta AU a Somalia

2022-04-07 10:04:37 CMG HAUSA

 

Babban sakataren MDD Antonio Guterres, a ranar Laraba ya yi maraba da matakin da kungiyar tarayyar Afrika ta dauka a baya bayan nan na kafa tawagar kiyaye zaman lafiya ta wucin-gadi a Somalia (ATMIS).

Cikin wata sanarwa, babban jami’in ya jaddada cikakken goyon bayan MDD ga kasar Somalia, da tawagar ATMIS, da dakarun tsaron kasar  Somaliya, a yakin da suke ci gaba da fafatawa da mayakan al-Shabab.

Sakataren MDDr ya bukaci dukkan abokan hulda su gaggauta samar da isassun kudaden da ake bukata ga tawagar ATMIS , da samar da jami’an tsaron kasar Somaliya don taimakawa ayyukan wanzar da zaman lafiya da tsaro.

Babban jami’in MDD ya bayyana aniyarsa na yin aiki kut-da-kut da kungiyar tarayyar Afrika, da gwamnatin kasar Somaliya, da dukkan abokan hulda, dake tallafawa jami’an tsaron kasar Somaliya wajen ayyukan tabbatar da zaman lafiya da tsaro a kasar. (Ahmad)