Za a jima ana tuna gasar Paralympic ta birnin Beijing
2022-04-07 20:30:39 CMG Hausa
Har yanzu masu fashin baki na ta bayyana irin gamsuwar su, da yadda gasar Olympics ajin masu bukata ta musamman, ko Paralympic ta lokacin hunturu ta Beijing ta gudana a bana, da irin nasarori da aka cimma yayin gasar.
A bangaren ‘yan wasan da suka shiga gasar daga kasar Sin, Guo Yujie ta ce za ta jima ba ta manta gasar nan ta 2022 ba. A matsayin ta na daya daga wadanda suka daga tuta, a rukunin ‘yan wasa Sinawa, yayin bikin bude gasar, kuma wadda ta lashe lambar zinari ajin mata a gasar biathlon, Guo ta ce "Muddin muka ci gaba da kwazo, komai mai yiwuwa ne", kuma wannan gasa ta birnin Beijing da aka kammala, za ta ci gaba da karfafa gwiwar karin mutane masu bukatar musamman, su shiga wasanni da za su iya canza rayuwar su, tare da karfafa jin kimar kan su.
Guo tare da sauran ‘yan tawagar wasan ta, da suka fafata a gasar dogon zango na wasan “skiing”, da “biathlon”, sun yi matukar shiri domin tunkarar gasar ta Beijing ta 2022, a yankin filin wasan dake Baiyin, inda suka yi horo, kafin nan ma, a watan Janairu sun yi horo a lardin Gansu na arewa maso yammacin kasar Sin.
Yayin wasannin da suka shiga, tawagar Sin ta gabatar da ‘yan wasa 33, domin shiga nau’oin wasanni 38 na “skiing”, da “biathlon” na dogon zango, sun kuma yi nasarar lashe lambobin zinari 11, da azurfa 8, da tagulla 11.
A nata bangare, Wang Hongwei mai shekaru 32 da haihuwa, wadda kuma manaja ce ta cibiyar horaswa, tana cikin tawagar kwararru a gasar ta Beijing ta 2022, a bangaren wasan “Alpine skiing” ko NTO.
Wang ta ce ta amfana sosai daga kwarewar da ta samu, a matsayin ta na mamba a NTO, wadanda suka kara mata kwarin gwiwa game da ba da gudummawar raya wasanni a nan gaba, musamman fannin tallafawa masu nakasa dake shiga wasanni a kasar Sin.
Wang ta ce "Yayin gasar “Paralympic”, an samar da kayan wasa da na amfani yayin wasannin, irin wadanda suka saukakawa ‘yan wasa yadda ya kamata, ga kuma ‘yan sa kai a kusa, domin bayar da tallafi ga duk mai bukata", ko shakka ba bu wadannan tanade-tanade sun martaba, tare da saukakawa ‘yan wasa masu bukatar musamman.
Wang, tare da ‘yan tawagar ta, sun taimaka wajen kammala gina kayan bukata na wasannin da aka gudanar a gasar, tun a karshen shekarar 2021, ciki har da masaukin ‘yan wasa, da wuraren cin abinci, da rufaffun dakunan horo dake cibiyoyin gasar.
A nata bangare kuwa, Wang Chenyang, wadda ta lashe lambar zinari a gasar ta Paralympics ajin wasan dogon zango na “skiing”, ta fara horo tun da wuri a cibiyar horo dake birnin Baiyin, ta kuma ce kayan da aka tanada suna da inganci matuka, sun kuma dace da matakin kasa da kasa.
A ‘yan kwanakin baya, tawagar Sin ta aike da wata wasika ta godiya ga cibiyar horon, bisa aiki tukuru da ta yi na samar da hidimomi masu inganci.
Wang Hongwei ta yi imanin cewa, mafi yawan kwarewar da ta samu, na da nasaba da yadda ta yi cudanya, da ba da hidima da masu bukata ta musamman a gasar ta Beijing ta 2022.
Wang Hongwei, ta ce "Ina da karfin gwiwar a nan gaba, zan jagoranci tawaga a cibiyar mu, wajen baiwa al’ummar mu masu bukatu ta musamman hidima, ta samun horo da shiga gasanni" Wang ta kara da cewa, abubuwan da suka wakana sun karfafa mata gwiwar cewa, nan gaba harkokin wasanni ajin nakasassu na Sin za su ci gaba da bunkasa.
Wasu alkaluma da gamayyar kungiyar masu bukata ta musamman ta Sin ta fitar, sun nuna cewa, tun daga shekarar 2016, gwamnatin Sin ta shirya gasanni ajin nakasassu har sau 6 a jere, inda adadin larduna da yankuna masu cin gashin kai, da manyan birane dake shiga wadannan wasanni sun karu daga 14 zuwa 31, kana adadin ‘yan wasa masu bukatar musamman sun karu daga 10,000 zuwa sama da 300,000.
Sin ta lashe lambobin yabo 61, a yayin gasar Beijing ta Paralympics da aka kammala, ciki har da zinari 18, adadin lambobin da suka dara na saura sassa da suka shiga gasar.
Game da hakan, Guo wadda a kwanan nan ta cika shekaru 18, ta ce "Ina fatan zan shiga gasa ta gaba, da za a gudanar a Italiya tare da yin nasarar lashe zinari ga kasar ta".
Shi kuwa dan wasan “Alpine skiing” daga kasar Argentina, a gasar ta Paralympic Enrique Plantey, wanda ya zo na 4 a gasar “giant slalom” ajin maza a gasar ta birnin Beijing a 2022, ya jaddada yadda gasar ta ba shi damar haduwa da mutane, da samun nishadi.
Plantey ya ce "Wasanni na da matukar amfani, suna taimakawa mutum fita daga gida, da haduwa da mutane. Dama ce ta baiwa mutum kuzari, kuma hanya ce ta nishadi da na zaba, bayan da na yi hadari, wato hadarin mota da ya rutsa da ni wanda ya haifar da shanyewar barin jiki na tun ina karami”.
Plantey ya ce a yau mutane masu bukatar musamman ana karfafa musu gwiwa, su fita waje su yi cudanya da sauran mutane yadda ya kamata.
Plantey ya kara da cewa "Ban taba fuskantar ko wace irin muzgunawa ba. Tun lokacin da na samu nakasa ina dan shekara 11 da haihuwa, na kuma yi sa’a ina rayuwa a muhalli da ya dace da yanayin da na samu kai na. Kaza lika na ji matukar dadin halartar gasar nan ta birnin Beijing”.