logo

HAUSA

An lamincewa tsohon shugaban Burkina Faso Marc Kabore ya koma gida

2022-04-07 11:00:42 CMG HAUSA

 

Gwamnatin rikon kwaryar kasar Burkina Faso ta amince tsohon shugaban kasar, Roch Marc Christian Kabore, wanda ake tsare da shi tun a ranar 24 ga watan Janairu, bayan wani juyin mulkin sojoji da ya hambarar da gwamnatinsa, a yanzu an lamince masa ya koma gidansa.

A cewar sanarwar, Kabore zai koma gidansa dake Ouagadougou babban birnin kasar a ranar Laraba, yayin da aka dauki kwararan matakan tabbatar da tsaron lafiyarsa.

A ranar 24 ga watan Janairu, sojojin kasar suka ayyana kawo karshen gwamnatin Kabore, bisa zarginsa da gaza magance matsalolin tsaro da suka dabaibaye kasar tun a shekarar 2015.

Tun daga wancan lokacin, yake tsare a hannu sabbin jami’an gwamnatin kasar, yayin da jam’iyyarsa ta (MPP), da sauran kungiyoyin shiyyar, kamar kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma (ECOWAS), suka bukaci a sake shi ba tare da gindaya sharruda ba. (Ahmad)