Sayarwa Taiwan makamai yana nuna cewa Amurka ce babban tushen tayar da rikici a duniya
2022-04-07 20:53:28 CMG Hausa
Kwanan nan, hukumomin Amurka sun yanke shawarar sayar da fasahohin makamai masu linzami na Patriot, wadanda suka kai darajar dalar Amurka miliyan 95 ga yankin Taiwan na kasar Sin. Wannan dai shi ne karo na uku da Amurka ta sayar wa Taiwan makamai, tun bayan da gwamnatin Amurkan mai ci a yanzu ta hau karagar mulki, kuma watanni biyu kacal ke nan tun bayan karo da ya gabata. Halin da take yi na sayar da makamai ga Taiwan akai-akai, ya nuna tunanin Amurka na hura wuta, da rashin amincewa, da tsoron cewa duniya ba za ta kasance cikin rudani ba.
Me ake kawo wa Taiwan sakamakon sayen makamai daga Amurka? Mazauna yankin ne kawai za su iya fahimta. Wasu masu amfani da yanar gizo sun yi nuni da cewa, “Amurka ba ta son zaman lafiya a mashigin tekun Taiwan”, kuma “Amurka ta kutsa kai ne don sake janyo kudi.” Wannan ya bayyana sosai, makircin siyasar Amurka na tayar da tarzoma, da yankar Taiwan a matsayin tunkiya mai kiba, da wadatar da masana’antun aikin sojan ta.
An amince cewa kasar Sin daya ce tak a duniya, kuma Taiwan wani yanki ne na kasar Sin, wannan tarihi ne na hakikanin gaskiya, wanda ba za a canja shi ba. A hakika dai, tsaron Taiwan ya dogara ne kan ci gaban dangantakar dake tsakanin gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan cikin lumana, ba wai sayen makamai daga Amurka ba. (Mai fassara: Bilkisu Xin)