An tona asirin Amurka na kulla makircin tada yakin cacar baka
2022-04-06 20:40:14 CMG Hausa
Rikicin kasar Ukraine, sabon tarko ne da kasar Amurka ta kafa a wannan karnin da muke ciki, kasancewar ta kasa mai kulla makarkashiyar tada yakin cacar baka, a wani yunkuri na hana ci gaban kasar Rasha, da taka birki ga kasashen Turai, ta yadda za ta kara nuna mulkin danniya a duk fadin duniya.
Kwanan nan, jakadan Amurka na karshe a tsohuwar tarayyar Soviet Jack Matlock, ya rubuta bayanin cewa, wannan shi ne rikicin da aka iya hasashe, kuma hakika an taba yin hasashen faruwarsa, amma rikici ne da aka tayar da gangan.
Sin kasa ce ta daban da Amurka take mayar da hankali a kan ta a cikin rikicin soja tsakanin Rasha da Ukraine. Kasar Sin ta sha jaddada cewa, ba ta son ganin irin halin da ake ciki yanzu, amma kasashen yammacin duniya, ciki har da Amurka sun rika shafawa kasar Sin bakin fenti, da matsa mata lamba, wajen sanya wa Rasha takunkumi.
Amurka tana yunkurin balle kasashen yammacin duniya daga kasashen Sin da Rasha, don su zama bangarorin biyu masu gaba da juna, al’amarin da ya zama ainihin ra’ayin yakin cacar baka.
Tashar intanet ta mujallar “The National Interest” ta Amurka, ta wallafa wani sharhi a kwanan nan, inda a cewar ta, gwamnatin Biden ta kan nuna ra’ayin yakin cacar baka a manufofin diflomasiyyar kasar, amma lokacin yakin cacar baka, ba lokaci ne mai kyau ba, a fannin raya huldodin kasa da kasa, lokaci ne da miliyoyin mutane suka rasa rayukansu a duk fadin duniya. A sabili da haka, bai dace Amurka ta ci gaba da tsunduma kanta, cikin wani yanayi na tunawa da nasarar da ta samu a lokacin yakin cacar baka ba. (Murtala Zhang)