logo

HAUSA

Kayan Aro Ba Ya Rufe Katara

2022-04-06 20:07:31 CMG Hausa

A ranar 5 ga watan Afrilun wannan shekara ne, al’ummar Sinawa suka gudanar da bikin Qingming, daya daga cikin bukukuwan Sinawa masu muhimmanci. Sanin kowa ne cewa, al’ada wani bangare ne na rayuwar bil-Adama. Kuma Sinawa na daga cikin al’ummomi a duniya da har yanzu ba su yi watsi da al’adunsu na gargajiya ba. Wannan shi yake nuna cewa, duk al’ummar da waye, ita ce ta ke rike al’adunta, riko na hakika

Daya daga cikin al’adun wannan biki mai dadadden tarihi na tsawon sama da shekaru 2,500, shi ne tsaftace kabarin magata, inda yayin da ake tsaftace kabarin magabata, a kan ajiye abinci da furanni a gaban kabarin, a kuma zubawa kabarin sabuwar kasa, har ma a dasa bishiya a gyafensa. Daga bisani a durkusa a yiwa mamaci addu’a. A zamanin da jama’a kan shafe kwanaki biyar zuwa goma suna wannan biki na Qingming.

Al’ummar Sinawa, mutane ne masu girmama magaba, abin da ke kara nuna muhimmancin wannan biki. Wannan ya kara tabbatar da cewa, Sinawa ba su manta da al’adunsu na gado wadanda suka gada daga kaka da kananni ba, kuma ba sa aron al’adun wasu ba.

Sai dai saboda shigowar zamani da wayewar kan al’umma, an dan samu wasu sauye-sauye a wannan al’ada, inda yanzu aka daina kona takardun kudi na jebu da aka saba yi a baya, saboda magance gurbata muhalli da yadda a wasu lokuta hakan ke haddasa gobara. Ana dai kona irin wadannan takardun kudi na jebu ne, da fatan wadanda suka mutun za su kasance cikin alheri da wadata.

Wani abu mai muhimmanci shi ne, lokacin Qingming lokaci ne na noma, domin a lokacin an fara dumi kana kasar da ta daskare ta farfado, don haka, a wannan lokaci, manoma kan dukufa kan aikin noma da fatan samun amfanin gona mai armashi a lokaci a kaka. Kana lokaci ne na yawon shakatawa.

A takaice dai, ya dace kowa ce al’umma ta martaba al’adunta na gargajiya, kamar yadda al’ummar Sinawa ke kiyaye duk wani nau’I na al’adunsu. Domin kayan aro aka ce ba ya rufe katara. Kuma guntun gatarinka, ya fi sari ka ba ni.(Ibrahim Yaya)