Rawar da Sin Da OIC za su taka wajen tabbatar da zaman lafiya a Duniya
2022-04-06 08:52:48 CMG Hausa
A kwanakin baya ne majalisar ministocin harkokin wajen kungiyar kasashe musulmi OIC, ta gudanar da taronta karo na 48 a birnin Islamabad na kasar Pakistan, inda a karon farko ya samu halartar mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi.
Karbar bakuncin ministan harkokin wajen kasar Sin da kungiyar ta yi, babbar alama ce dake cewa, suna goyon bayan ayyukan da kasar Sin ke yi na yaki da ta’addanci, haka kuma sun san hakikanin yanayin da yankin kasar Sin dake da rinjaye musulmi ke ciki.
Kamar yadda Wang Yi ya fada, wannan wani muhimmin bangare ne na huldar kasashe masu tasowa. A matsayin kasar Sin na babbar kasa mai tasowa cikin sauri a duniya, da kasashen kungiyar OIC na kasashe masu tasowa, hadin gwiwa a tsakaninsu abu ne mai matukar fa’ida, domin za su amfana da irin manufofi da dabarun kasar Sin na ci gaba.
Wang Yi, ya bayyana cewa, kasar Sin da kasashen musulmi, na da buri mai karfi na hadin gwiwa domin tabbatar da hadin kai da adalci da samun ci gaba, wadanda abubuwa ne da ake bukata a wannan lokaci da duniya ke fuskantar kalubale mabanbanta kana wasu kasashe ke kokarin rura wutar rikici da kawo rarrabuwar kawuna tsakanin al’ummomi.
Tun bayan barkewar annobar COVID-19, kasashen musulmi sun taimakawa kasar Sin, ita ma kasar Sin a nata bangaren, ta samarwa kasashen musulmi guda 50 tallafin alluran rigakafin COVID-19 biliyan 1.3 da sauran kayayyakin yaki da annobar.
Haka kuma, shawarar “ziri daya da hanya daya” ta kara bunkasa alakar sassan biyu. Ya zuwa yanzu, kasar Sin ta sanya hannu kan takardun hadin gwiwa da ta shafi shawarar da kasashen musulmi 54, baya ga kusan manyan ayyuka 600 da darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 400 da suka kulla. Kuma wannan hadin gwiwar ta amfanawa al’ummominsu. Sassan biyu suna koyi da juna, sun kuma kudiri aniyar kare mabambantan wayin kai duniya da ma bayar da gudummawa ga wayewar kan dan-Adam a tarihi.
Don haka, Wang Yi ya kara jaddada bukatar hada kai don kare ’yanci da muradu da cikakkun yankunansu da zabar hanyar bunkasuwa da ta dace da yanayin da suke ciki, da tabbatar da zaman lafiya da adalci da daidaito, samun nasara tare. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)