logo

HAUSA

Yi wa masu juna biyu allurar rigakafin COVID-19 yana iya kare jarirai sabbin haihuwa daga kamuwa da cutar

2022-04-06 07:52:49 CMG Hausa

 

Wani jaririn da aka haife shi kwanan baya a tsibirin Ibiza na kasar Spain ya zama jariri sabuwar haihuwa na farko wanda ke da kariyar annobar cutar numfashi ta COVID-19 a jikinsa bayan haihuwarsa a Spain, albarkacin mahaifiyarsa wadda aka yi mata allurar rigakafin cutar yayin da take da ciki. Masanan Spain sun shaida wa manema labaru cewa, lamarin ya bude sabon shafi na taimakawa jarirai samun kariyar cutar COVID1-9 ta hanyar yi wa mahaifansu mata allurar yayin da suke da ciki.

An yi wa mahaifiyar wannan jariri allurar yayin da take dab da haihuwa. Bayan haihuwar jaririn, an yi bincike kan jinin da aka diba daga cibiyarsa, inda aka gano cewa, yana da kariyar cutar ta COVID-19 tun bayan da aka haife shi. Wani jami’in hukumar lafiya ta kasa da kasa wato WHO ya yi nuni da cewa, jaririn yana da kariyar cutar COVID-19 kamar yadda aka yi masa allurar kai tsaye. Ko da yake ba a san tsawon lokacin da zai dauka yana kare shi daga kamuwa da cutar ba. Amma bayan haihuwarsa, ya samu kariya daga kamuwa da cutar.

Yanzu ba a tilasta yi wa masu juna biyu allurar rigakafin cutar COVID-19 a Spain ba. An ba da shawarar cewa, masu juna biyun sun fi fuskantar barazanar kamuwa da cutar ta COVID-19, don haka idan suna son a yi musu allurar, to, ba a hana yi musu ita ba.

Haka zalika kuma, likitoci masu kula da mata da mata masu juna biyu na Spain sun yi bayani da cewa, wani nazarin da aka gudanar kan illolin da cutar COVID-19 ke kawo wa masu juna biyu ya nuna cewa, a cikin jariran da masu fama da cutar ta COVID-19 suka haifa, wasu sabbin haihuwa da yawansu ya kai kaso 78 cikin dari ne suke da kariyar cutar a jikinsu.

Masana masu ruwa da tsaki sun yi bayani da cewa, idan an tabbatar da sakamakon nazarin, to, nan gaba muddin an yi wa masu juna biyu allurar rigakafin cutar COVID-19, idan babu kwayar cutar a ciki, to, za a ba da kariya ga masu juna biyun da ma jariransu sabbin haihuwa. A yawancin lokaci, idan mahaifa mata suna da kariyar cutar, to, ‘yan tayinsu za su samu kariyar ta hanyar uwar cibiya, ta haka jarirai sabbin haihuwa za su samu kariyar bayan an haife su. (Tasallah Yuan)