logo

HAUSA

Matsayar Kasar Sin dangane da batun Ukraine, ta jaddada matsayinta na babbar kasar da ta san ya kamata

2022-04-05 19:18:16 CMG

Kasar Sin ta sake jadadda matsayarta game da batun Ukraine da Rasha. Inda ta nanata cewa, bata neman cimma wani muradi na son kai a siyasar duniya dangane da batun, haka kuma, bata nuna halin ko in kula, bare kuma ta nemi kara rura wutar rikicin. Hakika, wannan ya sake fito da matsayin kasar Sin na babbar kasa da a kullum take kira da hawa teburin sulhu don tattaunawa da zummar samun maslaha, maimakon haddasa fito na fito.

Kasar Sin ta bayyana haka ne ta bakin mamban majalisar gudanarwar kasar kuma ministan harkokin wajenta Wang Yi, yayin da yake tattaunawa ta wayar tarho da ministan harkokin wajen Ukraine Dmytro Kuleba.

Tattaunawar wadda irinta ce ta biyu tun bayan barkewar rikici tsakanin Rasha da Ukraine, ya kara tabbatar da matsayin kasar Sin mai sanin abun da ya kamata, domin ta tsaya ne tsayin daka wajen tuntubar kowanne bangare da zummar lalubo bakin zaren rikicin maimakon nuna bangarannci ba tare da bada wata gudunmuwa na kawo karshen fitinar ba.

Kamar yadda Wang Yi ya bayyana, ainihin abun da Sin take sa rai game da yanayin Ukraine shi ne zaman lafiya. Wato bata da wani buri da ya wuce zaman lafiya a duniya. Ingiza tattauanwar zaman lafiya da take yi tsakanin bangarorin biyu, manuniya ce cewa bata da wani abu da take burin samu daga rikicin. Kasar Sin ta sha nanata cewa, bata da wata riba daga faduwar wata kasa a duniya. Wannan haka yake, domin shaidu sun nuna cewa, hanyar ta na neman ci gaba, ya bambanta da na sauran manyan kasashe, domin tana raya kanta ne bisa nata tsarin a cikin gida ba tare da takurawa ko mulkin mallaka ba. Lamarin da ba sai an fada ba, ya kai ta ga samun ci gaba cikin sauri har take da babban matsayin a idon duniya. (Fa’iza Mustapha)