logo

HAUSA

An haramta shuka tsiron Poppy a Afghasnitan

2022-04-05 20:53:24 CMG Hausa

Gwamnatin wucin gadin kasar Afghasnitan ta fitar da sanarwar cewa, bisa ga umurnin da jagoran Taliban na kasar Moulavi Haibatullah Akhunzada ya bayar, za a haramta shuka tsiron da ake kira Poppy a Turance, wanda ake samar da hodar iblis da shi, da ma cinikinsa a fadin kasar.(Lubabatu)