logo

HAUSA

Aliyu Uba Taura: Karatun da na yi a kasar Sin yana taimaka min a aikina a Najeriya

2022-04-04 21:56:14 CMG Hausa

Aliyu Uba Taura, wani dan asalin Jigawar Najeriya ne, wanda ya shafe shekaru da dama yana karatu a kasar Sin, musamman biranen Beijing da Tianjin. A halin yanzu, Malam Aliyu Uba yana aikin koyarwa a fannin kimiyyar na’ura mai kwakwalwa, wato computer science a turance, a jami’ar Kaduna dake arewacin Najeriya.

A yayin zantawarsa da Murtala Zhang, Malam Aliyu Uba ya bayyana ra’ayinsa, kan bambancin yanayi karatu tsakanin Najeriya da kasar Sin, da fahimtarsa game da al’adun gargajiya na kasar.

A karshe, malam Aliyu ya bayyana kyakkyawan fata, gami da shawararsa ga ‘yan uwansa al’ummar Najeriya, musamman matasa. (Murtala Zhang)