logo

HAUSA

Luo Haixiang dake mai da hankali kan kare lafiyar mazauna kauyan da ke cikin tsaunuka a cikin sama da shekaru 20

2022-04-03 19:09:38 CRI

Luo Haixiang, likita daya tilo dake aiki a kauyen Baigu da ke garin Yunwu na lardin Guizhou dake kudu maso yammacin kasar Sin, ta fara karatun likitanci tun ba ta kai shekara 16 ba. Ta shafe shekaru 36 tana kai-koma tsakanin tsaunuka, a kokarin samar da jinya da ceton rayuka, ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen gabatar da sabbin hanyoyin haihuwa ga mata da kuma yiwa jarrirai rigakafi, inda jariran da aka haifa a karkashin taimakonta sun wuce 100.

Yanzu haka, yawan mata masu juna biyu da suka haihu a asibiti a kauyen Baigu ya kai 100%. Luo Haixiang, wadda shekarunta na haihuwa suka wuce 50, har yanzu tana gudanar da wannan muhimmin aiki a kowace rana, domin kiyaye lafiyar mazauna wurin.

A kauyen Baigu dake cikin tsaunukan lardin Guizhou a shekaru sama da 10 da suka gabata, makomar mata ko da yaushe ba ta rabuwa da abubuwa biyu, wato aure da haihuwa.

A tsakiyar shekarun 1980, wata mata dake kauyen ta samu ciki karo na hudu. Lokacin da take da juna biyu, tana nuna alamun tana da hawan jini. Don haka, Luo Haixiang ta sha lallashinta tana cewa, “Wannan yanayin na da hadari sosai, dole ne ki je asibiti.” Sannu a hankali, wannan mata mai juna biyu ta canja ra’ayinta, amma iyalanta sun tsaya kan cewa, “Ba ta gamu da wata matsala ba a lokacin da ta haife ’ya’ya guda uku na farko, likita Luo, wannan ba abin damuwa ba ne.”

A ranar da ta fara nakuda, ta sha wuyar haihuwa, inda ta zubar da jini da yawa, abin da ya sa iyalinta suka nemi Luo Haixiang. Amma, babu abin da za ta iya yi, saboda suna zaune a wani tsauni mai tsayi, babu isasshen lokacin da za a kai ta asibiti. Illa a jira lokacin mutuwar matar da jaririn dake cikinta.

A ranar da aka kona gawar matar a kan dutsen, mutanen kauyen da danginta sun kalli Luo Haixiang, ta nade hannayenta tana goge hawaye, Suna fadin cewa, “Haka kakanninmu suka yi, ba ta ciwannan jarabawar ba, wannan ita ce makomarta"

"Haka ya kamata makomar mace ta kasance? Me ya sa makomarsu ba za ta kasance a hannunsu ba a wannan muhimmin lokaci na samun ciki da haihuwa!" Shekaru da yawa bayan faruwar lamarin, Luo Haixiang har yanzu tana tunawa da bacin ran da take ji a wancan lokaci "daka mata wuka".

Kusan babu wata macen da ke iya kubuta daga wannan kaddara. Ba maza kadai ba, mata da yawa su ma sun zama “magada” irin wannan kaddarar, sun ki su canja tsohuwar al’ada.

A cikin shekaru fiye da goma da suka gabata, Luo Haixiang ta sha yin mafarkin wancan matan da ta mutu sanadiyar haihuwa. Don haka, ta lashi takobin canza wannan al’ada kuma mai kula da makomar matan dake zama a cikin tsaunuka.

A shekarar 1984, domin bunkasa aikin likitanci da kiwon lafiya a yankunan karkara, kasar Sin ta bukaci kowane gari da ya gabatar da wani dalibi ko daliba dake karatu a makarantar sakandare, don karanta fannin kiwon lafiya a makarantar koyon harkar kiwon lafiya dake gundumar yankin. A bisa shawarar tsohon shugaban asibitin gundumar, Luo Haixiang, wadda ba ta wuce shekaru 16 ba, ta samu damar koyon likitanci. Ta ce, a baya ta nuna damuwa, domin ba ta taba yin tafiya mai nisa ba, kuma ba ta da tushen aikin likitanci, shin za ta iya koya yadda ya kamata kuwa? Amma, karin gwiwar da ta samu daga mahaifinta, da kudin balaguro da na abinci da babban yayanta ya samar mata, sun taimakawa Luo Haixiang matuka.

Bayan shekara daya da rabi tana koyon dokokin aikin likitanci, tare da samun horo na rabin shekara a cibiyar kiwon lafiya ta gundumar, Luo Haixiang ta sami takardar shaidar kammala karatu. Ta koma kauyensu cikin farin ciki, don zama lokita a cibiyar kiwon lafiya ta gundumar.

Bayan ‘yan kwanaki da fara aiki, tsohon sakataren gundumar ya gaya wa Luo Haixiang cewa, “Me ya sa aka ce miki ki yi karatun likitanci, bayan ‘yan shekaru, za ki bar kauyen Baigu domin ki auri wani, wannan ai bata wata kyakkyawar dama ce.”

Game da haka, Luo Haixiang ta ba da amsa nan da nan, “Zan zauna a kauyenmu, ba zan yi aure a wani wuri ba!”

Da ya ji haka, sai tsohon shugaban asibitin gundumar ya yi dariya, yana cewa, "Idan kin hadu da mutumin kirki a wani kauye, ba za ki aure shi ba?"

Amma sai Luo Haixiang ta amsa da karfi tana cewa, "Duk girman wannan kauyen namu, ba zan samu mutumin kirki ba?".

Bayan ya kalli irin hali na Luo Haixiang, sai tsohon shugaban asibitin ya gaya wa wannan likitar kauyen mai shekaru 17 da haihuwa, irin muhimmin "nauyin" dake wuyanta.

A wancan lokacin, kasar Sin na kokarin aiwatar da sabuwar hanyar haihuwa da kuma shirin yin rigakafi, domin rage mace-macen mata masu juna biyu da kuma jarirai, kauyen Baigu yana daya daga cikin yankuna masu nisa, babu ruwan sha, wutar lantarki da hanyoyin mota, abin da ya sa mazauna kauyen zama a cikin wani yanayi na kunci, don haka suna da ra'ayi da tunani irin na mazan jiya da kuma tsayawa tsayin daka kan al’ada. Balle ma su karbi "sabuwar hanyar haihuwa", wato likitoci su taimaka wa mata masu juna biyu wajen haihuwa. Har ma mazauna kauyen suna ganin cewa, samun ciki wani abun kunya ne.

Tsohon shugaban asibitin ya gabatar da aikin da Luo Haixiang za ta aiwatar, wato "Dole ne a sanya mutanen kauye suka yarda da ‘sabuwar hanyar haihuwa’, kuma ma’aunin dukkan fannoni zai kai fiye da 85%." Game da haka, Luo Haixiang ta ba da amsar cewa, "Babu matsala, zan kammala aikin yadda ya kamata!"

Amma, ko shakka babu, ba ta damu da wahalar da za sha a aikin ba. To, wadanne matsaloli take fuskanta a wajen aiki? Ta yaya ta kawar da su? Za mu kawo muku amssoshin wadannan tambayoyi a shirinmu na mako mai zuwa. Da fatan za ku kasance tare da mu.