logo

HAUSA

Kamfanin Sin yana gaggauta ayyukan titinan mota a Najeriya

2022-04-03 16:53:48 CMG Hausa

Gwamnatin Najeriya ta yaba yadda ayyukan gina manyan hanyoyin mota da suka hade sassan arewaci da kudancin kasar ke gudana cikin sauri, wanda kamfanin kasar Sin ke gudanarwa duk kuwa da kalubalolin da aikin ya fuskanta a matakin farko na farawa.

Karamin minsitan ayyuka da gidaje na kasar, Mu'azu Sambo, wanda ya jagoranci tawagar jami’an gwamnati da na kasashen waje daga wasu kasashen Afrika wadanda ke ziyarar duba aiki, yace, aikin gina tagwayen tituna na Abuja zuwa Keffi, da na Keffi zuwa Akwanga zuwa Lafia zuwa Makurdi, dake shiyyar tsakiyar Najeriya, zasu taimaka wajen magance wasu daga cikin matsalolin tattalin arziki, da na zamantakewa dake damun al’ummar Najeriya.

Aikin, wanda kamfanin gine-gine na China Harbor Engineering Company (CHEC), ke gudanarwa, an kasa shi zuwa bangarori hudu, wanda ya kai jimillar kilomita 220.

Bisa yarjejeniyar aikin, gwamnatin Najeriya zata samar da kashi 15 bisa 100 na kudaden aikin, yayin kashi 85 na kudaden aikin bankin shigi da fici na kasar Sin ne zai samar dasu.

Sambo ya bayyana cewa, idan aikin ya kammala, hanyoyin zasu taimaka musamman wajen bunkasa harkokin tattalin arziki da zaman rayuwar al’umma, kana zasu taimaka wajen magance matsalolin tsaro da kalubalolin a fannin sufuri a titinan mota a sassan kasar.

Yace aikin ba kawai zai inganta harkokin sufuri a kasar Najeriya ba ne, har ma zai hade sassa daban daban na Afirka ta hanyar hada titinan mota a tsakanin kasashen yammacin Afrika, da tsakiya, da arewacin nahiyar, lamarin da zai yi matukar inganta yanayin titunan mota a shiyyar.

Ya kara da cewa, sama da guraben ayyuka na kai tsaye 2,00O aikin gine-ginen titinan ya samar.(Ahmad)