logo

HAUSA

Bai dace Amurka ta sake shaidawa duniya cewa “wai barawo ne ke kiran a kama barawo” ba

2022-04-03 17:41:12 CMG Hausa

‘Yan siyasar Amurka sun sake hada baki tare da kafafen yada labaran kasashen yammacin duniya. Kwanan nan ne jaridar The Times ta kasar Birtaniya ta ruwaito wata majiya daga hukumar leken asirin Amurka dake cewa, wai kafin kasar Rasha ta dauki matakan soja na musamman kan kasar Ukraine, kasar Sin ta kaddamar da “gagarumin hari ta kafar sadarwar intanet” kan na’urorin aikin soja da na makamashin nukiliya na Ukraine. Har ma jaridar ta kara da cewa, hukumar tsaron kasar Ukraine ce ta yi zargin.

Wannan zance karya ce tsagwaronta! Hukumar tsaron kasar Ukraine ta karyata wannan labari ta hanyar kafofin sada zumunta da dama, inda ta bayyana cewa, ba ta taba samar da irin wannan labari ba ga wata kafar yada labarai, kana ba ta da masaniya, kuma ba ta taba gudanar da bincike kan wannan batu ba. Ta kara da cewa, “sakamakon binciken” da jaridar The Times ta kasar Birtaniya ta fitar ba shi da alaka ko kadan da hukumar tsaron kasar Ukraine.

Hakika, idan mun ambaci batun kai farmaki ta kafar sadarwar intanet, Amurka ta yi kaurin suna fiye da sauran kasashe, amma kasar Sin ta fi jin radadi a jikinta a wannan fanni. Bisa binciken da cibiyar kula da ayyukan gaggawa ta hadakar na'urorin kwamfuta ta kasar Sin da aka fi sani da CNCERT/CC ta gudanar, tun a karshen watan Fabrairun bana, ya zuwa yanzu, ta hanyar kai farmaki kan na’urori masu kwakwalwa dake kasar Sin, akwai wasu kungiyoyin kasashen ketare wadanda suka rika kai farmaki kan kafofin sadarwar intanet na kasashen Rasha da Ukraine da kuma Belarus. Kana, akasarin farmakin daga Amurka ne aka kaddamar.

Kwararan shaidu na nuna cewa, rahotannin da ake ta yayatawa game da farmakin da kasar Sin ta kaiwa kasar Ukraine ta hanyar intanet, karya ce tsagwaronta, kana, wata sabuwar dabara ce da kasashen yammacin duniya musamman Amurka ke amfani da ita wajen shafawa kasar Sin bakin fenti. Abun lura shi ne, bayan barkewar rikicin soja tsakanin Rasha da Ukraine, wasu ‘yan siyasar Amurka sun hada baki da kafafen yada labarai don yayata labaran bogi game da kasar Sin. Manazarta na ganin cewa, Amurka na iya yunkurin bata sunan kasar Sin, da kawo cikas ga alakar Sin da Rasha, da zummar cimma karin muradun siyasa daga rikice-rikicen duniya. (Murtala Zhang)