Kawar da rashin tabbaci a duniya ta hanyar kyakkyawar huldar Sin da EU
2022-04-02 21:10:50 CMG Hausa
Da yammacin ranar 1 ga watan Afrilu, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da shugaban majalisar kungiyar tarayyar Turai Charles Michel, da shugabar hukumar gudanarwar EU, Ursula von der Leyen, ta kafar bidiyo a Beijing.
Inda shugaba Xi ya yi tsokaci cewa, “Kamata ya yi Sin da kungiyar tarayyar Turai EU, su kasance a matsayin wasu manyan ginshikai biyu wajen tabbatar zaman lafiyar duniya, da kuma kai dauki kan yanayin rashin tabbaci na halin da duniya ke ciki ta hanyar kyakkyawar huldar dake tsakanin Sin da EU."
Wannan shi ne batu na gaskiya, da kuma tattaunawa mai zurfi tsakanin shugabannin Sin da EU. Bangarorin biyu ba kawai suna son zurfafa kyakkyawar fahimtar dake tsakaninsu ba ne, har ma sun cimman matsaya kan muhimman batutuwa da dama, lamarin da ke isar da wani muhimmin sako ga duniya dake nuna bukatar yin hadin gwiwa da juna don tabbatar da zaman lafiya da ci gaban duniya. A daidai lokacin da annobar cutar COVID-19 da rikice-rikicen shiyyoyi ke ci gaba da bazuwa, wadannan sakonni suna da muhimmanci kuma suna da matukar tasiri wajen kawar da rashin tabbaci din da duniya ke fuskanta. (Ahmad)