Bikin cika shekaru 40 da barkewar yakin Falklands
2022-04-02 18:57:50 CMG Hausa
Tun a karni na 19, tsibiran Malvinas dake kasar Argentina suka fuskanci mamayar Turawan mulkin mallaka na kasar Birtaniya. A ranar 2 ga watan Afrilu na shekarar 1982, Argentina ta gwabza yaki da Birtaniya domin kwace iko da yankunanta na Falklands. Yakin da aka kwashe kwanaki 74 ana gwabzawa, kuma daga karshe Birtaniya ta yi nasara. Ranar 2 ga watan Afrilu na bana ta kasance ranar bikin cika shekaru 40 da barkewar yakin Falklands. Ko da yake, yakin ya riga ya shude, sai dai ba abu ne da za a iya goge shi a tarihin al’ummar kasar Argentina ba, musamman gwarazan kasar Argentinan da suka fafata a yakin.(Ahmad)