logo

HAUSA

Rwanda ta kaddamar da cibiyar bunkasa sabbin fasahohin zamani

2022-04-01 14:19:02 CMG Hausa

A ranar Alhamis kasar Rwanda ta kaddamar da cibiyar raya masana’antun zamani wato (C4IR) a takaice.

An kafa cibiyar da nufin bunkasa masana’antun zamani, don samar da sauye sauye game da hanyoyin gudanar da rayuwar dan adam, da sauya makomar ci gaban bil adama a nan gaba ta hanyar kirkirar sabbin fasahohin zamani.

A yayin kaddamar da cibiyar, shugaba Paul Kagame na Rwanda yace, “yadda muke rayuwa, da yadda muke aiki, da mu’amalarmu da juna, zai cigaba da gudana bisa tsarin ci gaban fasahohin zamani. Sai dai tsarin kula da alkaluma ba su tafiya daidai da sauye sauyen da aka samu na fasahohin zamani. Don haka, ni kaina, na yabawa cibiyar bisa yadda take taimakawa ci gaban Rwanda wajen adana bayanai na daidaikun mutane da tsaronsu.”

Crystal Rugege, shine zai kasance a matsayin manajan daraktan cibiyar na farko.

A lokacin kaddamar da cibiyar, shugaban dandalin WEF, Borge Brende, yace, cibiyar bunkasa masana’antun zamani zata taka muhimmiyar rawa wajen cimma muradun kasar Rwanda na zama kasa mai matsakaicin cigaban tattalin arzikin nan da shekarar 2035.(Ahmad)