logo

HAUSA

QATAR 2022: Ghana Ta Hana Nigeria zuwa Kofin Duniya

2022-03-31 17:15:22 CMG HAUSA

Kofin Duniya: Italiya Ta Rasa Gurbi

A zagayen kusa da karshe na wasannin fitar da gwanayen da za su buga kofin kwallon kafa na duniya a shekarar 2023, kasar Italiya ta kwashi kashin ta a hannun kasar Macedoniya. Wanda hakan ke nufin Italiyar ba za ta je Gasar cin kofin duniya ba kenan.

 

Da yammacin jiya Alhamis ne tawagar Macedoniya ta buge ta Italiya da ci 1 mai ban haushi. A yayin da kasar Portugal kuma ta lallasa Turkiyya da ci 3 da 1. A zagayen karshe kuwa Portugal za ta kara ne da Macedoniya don fitar da gwani tilo.

 

QATAR 2022: Ghana Ta Hana Nigeria zuwa Kofin Duniya

Tawagar ‘yan wasan Super Eagles ta Nigeria ta kasa samun tikitin zuwa gasar cin kofin duniya da kasar Qatar zata karbi Bakunci a wannan shekarar.

A wasan farko dai da suka fafata a birnin Kumasi na Ghana kasashen biyu sun tashi wasa babu ci yayinda aka tashi 1-1 a wasan da suka fafata a daren yau.

Da wannan sakamakon, kasar Ghana ta samu tikitin zuwa gasar cin kofin duniya inda zata wakilci yankin Afirka.

 

Nigeria dai ta samu nasarar zuwa gasar cin kofin duniya da aka buga a kasar Russia a shekarar 2018.

Nigeria ta kasa samun tikitin ne bayan tashi wasa 1-1 da tawagar kasar Ghana a wasan da suka fafata a filin wasa na Moshood Abiola dake babban birnin tarayya Abuja.

 

Baya ga wasan Nijeriya da Ghana, Jadawalin wasannin neman tikitin halartar gasar cin kofin Duniya da za ta gudana a Katar ya nuna cewa Masar da Senegal za su sake kece raini a cikin watan Maris, inda kowace kasa za ta yi tattaki zuwa gidan abokiyar hamayyarta.

A sauran wasannin neman tikitin zuwa gasar ta cin kofin duniya a Katar, Kamaru za ta kara da Algeria, sai Mali da Tunisia, sai kuma Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo da za ta fafata da Morocco.

 

Kamar yadda yake a dokar Fifa, kasashe biyar daga nan nahiyar Afirka ne dai za su wakilci yanking aba daya a gasar wadda za’a fafata tsakanin kasshe 32 kamar yadda ake tsarawa duk shekara.

 

Ba Mu Fid Da Rai Da Lashe Gasar La Liga Ba, Cewar Xavi

Mai horar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Xavi Hanandez ya ce yanzu kam yana da kwarin gwiwar shiga tseren lashe kofin La Liga bayan nasararsu kan Real Madrid da kwallaye 4 da banza.

 

Nasarar ta Barcelona a ranar Lahadi shi ke nuna yadda kungiyar ta buga wasanni 12 zuwa yanzu ba tare da an yi nasarar doke ta ba, lamarin da Xavi ke cewa ta yiwu sun zo a makare ne amma su iya lashe kofin gasar.

A cewar Xavi Barcelona ta doka wasan ne tamkar a gidanta ta yadda ta kakkange ko’ina fiye da Real Madrid ta kowacce fuska, ya na mai cewa da sun samu dama da za su iya kara yawan kwallayen da akalla biyar zuwa 6 cikin sauki.

Shi ma dai dan wasan baya na Barcelona Gerard Pikue ya yi ikirarin cewa kungiyar ta sa ta dawo da karfinta domin yin gogayya da Real Madrid bayan nasarar ta jiya da ke matsayin mafi girma da kungiyar ta samu a wasannin baya-bayan nan. Real Madrid wadda ta yi naasara a haduwar El Classico 5 a baya-bayan nan wannan ne karon farko da ta ke shan kaye hannun babbar abokiyar hamayyarta, sai dai har yanzu ita ke jagoranci da tazarar maki 9 tsakaninta da Sebilla mai biye da ita yayin da ake da sauran wasanni 9 gabanin karkare kakar.

 

Arsenal Ta Shiga Zawarcin Hazard

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal na shirin fara tattaunawa da Real Madrid ta Sifaniya domin sayen dan wasanta na gaba Eden Hazard, a wani yunkuri na magancewa matsalar ‘yan wasan gaba da kungiyar ke shirin yi, dai dai lokacin da dan wasan na Belgium ya gaza bayar da gudunmawa a La Liga.

 

Tsohon dan wasan na Chelsea mai shekaru 31 ya gaza bayar da gudunmawar da aka yi hasashen zai bayar a Real Madrid tun bayan sayensa a kakar wasa ta shekara ta 2018 a kan kudi yuro miliyan 88 da rabi. Zuwa yanzu wasanni 65 kadai ya bugawa Real Madrid a tsawon shekara biyu da rabi da ya shafe a kungiyar mai buga gasar La Liga, sai dai wasu rahotanni sun bayyana cewa Arsenal na shirin tayin tsohon tauraron na Chelsea da ya dage kofunan firimiya biyu, sai dai Hazard dan Belgium na da sauran shekaru biyu da rabi a kwantiragin shekaru 5

da ya kulla da Real Madrid A 2018.

A bangare guda Arsenal na son sayen Hazard ne don cike gibin da Pierre-Emeric Aubameyang ya haifar mata bayan raba gari da kungiyar zuwa Barcelona sannan wasu bayanai na cewa baya ga Arsenal akwai kuma kungiyar kwallon kafa ta Newcastle United da ke zawarcin Hazard.

 

 

Sevilla Da Barcelona Na Zawarcin Umar Sadik Na Nijeriya

Kungiyar kwallon kafa ta Sevilla ta fara shirye-shiryen daukar dan wasan gaban Nijeriya da Almeria Sadik Umar kamar yadda wasu rahotanni daga kasar ta Sipaniya suka ruwaito a saiyar jiya.

 

Yanzu haka kungiyar da ke birnin Sebille na zaune ne a mataki na biyu a teburin gasar La Liga kuma Sevilla ta ce Sadik ne sahun gaba cikin ‘yan wasan da ta ke shirin saye da zarar an kammala kakar da ake ciki da dama ta kusa karewa.

 

Sai dai irin yadda ta rike wuta da cin wasanni, akwai yiyuwar Sevilla ta samu zuwa gasar zakarun turai a badi, wanda hakan zai bai wa dan wasan damar kara nuna kansa a idon duniya.

To amma akwai alamun Sevilla ta fuskanci abokan takara domin kuwa tun kafin su shiga nemansa rahotanni sun nuna cewa Barcelona tuni ta fara batun kulla ciniki da Almeria domin sayen dan wasan.

 

Sadik Umar ya koma Almeria da ke mataki na biyu a Spain da ake kira ‘Segunda dibision’ daga Partizan Belgrade da ke Serbia a watan Octoban shekara ta 2020, kuma tun bayan komawarsa kungiyar ya zama kashin bayanta.

 

A kakar da ta wuce Sadik mai shekaru 25 ya ci kwallaye 20 a wasanni 38 da ya bugawa kungiyar ta Almeria, duk da ba su samu zuwa gasar La Liga ba kuma kawo yanzu tuni ya ci kwallaye 11 a bana cikin wasanni 24 da ya buga.

 

Irin wannan bajinta ce ta ja hankalin Sevilla har ta yadda za ta biya kudin kwance yarjejeniyar sa da Almeria don ta kulla wata sabuwa da shi kuma dan wasa Sadik Umar yana da yarjejeniya ne da Almeria daga nan zuwa shekara ta 2025.