logo

HAUSA

Wajibi Ne Amurka Ta Dakatar Da Rura Wuta Tsakanin Rasha Da Ukraine

2022-03-31 11:18:51 CMG Hausa

Ranar 29 ga wata, an kammala shawarwarin zagaye na 5 tsakanin kasashen Rasha da Ukraine, kamar yadda ministan harkokin wajen kasar Turkey Mevlut Cavusoglu ya ce, an fi samun ci gaba a yayin shawarwarin na wannan karo.

An ruwaito cewa, a yayin shawarwarin, kasashen 2 sun cimma daidaito kan kasancewar Ukraine a matsayin kasa ’yar ba ruwanmu har abada, da yin watsi da shirin shiga kawacen soja, yayin da Rasha ta yarda da shigar Ukraine cikin EU, da daukar matakan sassauta rikici a tsakaninta da Ukraine, kana ana sa ran shugabannin kasashen 2 za su gana da juna.

Albarkacin ci gaban da aka samu, kasuwannin hannayen jari na kasashen Turai da Amurka sun samu hauhawa, lamarin da ya nuna cewa, kasashen duniya na jin dadin kyautatuwar halin da ake ciki a tsakanin Rasha da Ukraine. Amma Amurka, wadda ke ta da rikicin, ba ta ji dadin hakan ba, ba ta yi maraba da ci gaban ba. A daidai ranar da aka samu ci gaban, Wally Adeyemo, mataimakin ministar kudin Amurka ya ce, kasarsa da kawayenta sun shirya sanya wa Rasha sabon takunkumi a wasu muhimman sana’o’i, a kokarin lalata karfinta na ta da yaki. Tuni kuma shugaba Joe Biden na Amurka ya gana da shugabannin Birtaniya, Jamus, Faransa da Italiya ta waya, inda ya tsai da kudurin ci gaba da mara wa Ukaine baya, ciki hadda kara ba ta makamai.

Yayin da aka samu ci gaba a yayin shawarwarin Rasha da Ukraine, Amurka ta ci gaba rura wuta a tsakaninsu, ta hanyoyin rika bai wa Ukraine makamai, da kara sanyawa Rasha takunkumi. Abin da Amurka ta yi ya sake nuna cewa, ita ce mafi haifar da barazana ga zaman lafiya da tsaro a duniya. Wajibi ne ta dakatar da ta da yake-yake nan da nan. (Tasallah Yuan)