logo

HAUSA

Amurka ta yi dariya

2022-03-31 18:20:54 CMG Hausa

Kamala Harris, mataimakiyar shugaban kasar Amurka, ta bushe da dariya, a yayin da aka tambaye ta, ko Amurka za ta karbi wasu ‘yan gudun hijirar kasar Ukraine, a yayin ziyararta a kasar Poland a kwanan baya.

Jami’ar ta yi dariya kawai ba tare da ba da amsa ba, kuma hakan ya jawo mata suka, ganin yadda bai dace ba musamman a kan batun ‘yan gudun hijira a mayar da abun raha. Gaskiya bai dace ba, amma kasancewar Amurka wadda ta fi cin moriya a rikicin da ke tsakanin Rasha da Ukraine, lallai akwai abun da zai hana ‘yan siyasarta su yi dariya?

A matsayinta na wadda ta ta da rikicin, Amurka ba ta shiga yakin kai tsaye ba, don haka babu hasarorin rayuka, da ma hadarin hare-hare a gare ta, amma kuma ta lalata huldar da ke tsakanin kasashen Turai da Rasha, tare da dakushe karfin Rashan, har ma ta kai ga karfafa manufar Amurka na wanzar da mulkin danniya. Babu shakka, ita ce ta fi cin nasara a yakin. Ban da haka, ta hanyar fitar da makamanta ga Ukraine, masana’antun samar da makamai na kasar sun ci mummunar riba.

“Tun lokacin da rikici ya barke tsakanin Rasha da Ukraine, a cikin ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon, da “K Street” wato wurin tarukan kamfanoni masu janyo ra’ayi na Washington, da masana'antun samar da kayayyakin soja, da kuma cikin ginin Capitol, ana can ana ta shan barasha don murna!"  Kamar yadda Franklin C. Spinney, tsohon jami'in ma'aikatar tsaron Amurka ya yi tsokaci a baya-bayan nan, hakan ya nuna cewa, Amurka ce ta fi kowa cin moriyar fada tsakanin Rasha da Ukraine.

Me ke faruwa ga Ukraine da Rasha kuma? Ukraine da ta kasance kasa kyakkyawa, amma ga yadda yaki ya ji wa kasar munanan raunuka, da ma yadda rikicin ya raba al’ummar kasar da muhallansu. Alkaluman da MDD ta samar sun yi nuni da cewa, ya zuwa ranar 20 ga wata, rikicin ya tilasta kusan kaso 1/4 na al’ummar kasar tserewa daga gidajensu.

A sa’i daya kuma, bayan aukuwar rikicin, Amurka da sauran kasashen yamma, sun kakkaba wa Rasha takunkumai masu tsanani, wadanda suka shafi fannonin hada hadar kudi, da ciniki, da siyasa, da ayyukan soja da sauransu, har ma itatuwa da kyanwa na kasar ma ba su samu damar tsira daga takunkuman ba. Babu shakka, Rasha na fuskantar babban matsi a sakamakon takunkuman. Ma iya cewa, Rasha da Ukraine babu wadda ta ci nasara a rikicin.

Sakamakon rikicin kuma, ‘yan kasar Ukraine da yawa sun tsere zuwa kasashen Turai makwabta, don haka, matsalar kula da ‘yan gudun hijirar, ta zama abin da ke ci wa kasashen Turai tuwo a kwarya. Ban da haka, kungiyar tarayyar Turai na dogara sosai ga Rasha wajen shigowa da makamashi, amma takunkuman da kasashen yamma suka kakaba wa Rashan sun haifar da hauhawar farashin makamashi a kasashen Turai. Ga shi kuma da ana yiwa Ukraine kirarin “rumbun hatsi na Turai”, ga ma tasirin da hauhawar farashin makamashi ke haifarwa, farashin abinci ma na dada karuwa a kasashen Turai.

A sakamakon dunkulewar tattalin arzikin duniya, matsalar makamashi da abinci a sanadin rikicin da ke tsakanin Rasha da Ukraine ma, ta shafi sauran sassan duniya cikin sauri, wadda ta haifar da barazana ga farfadowar tattalin arzikin duniya, da ma kwanciyar hankalin al’umma. Misali, akwai kasashen Afirka da dama da ke dogara ga shigowa da hatsi daga Rasha da Ukraine, don haka rikicin ya tsananta batun samar da isashen abinci a kasashen Afirka. A Nijeriya kuma, matsalar karancin mai a sakamakon hauhawar farashinsa, tana haifar da matsaloli ga rayuwar al’ummar kasar.

Lallai, duk wanda ya san tarihi, zai gane cewa, Amurka ta saba da yin abin da take yi a rikicin Rasha da Ukraine, wato a takaice, za ta yi duk abin da zai amfane ta, ba tare da kula da me al’ummar sauran kasashe za su biya sakamakon rikicin ba.

Sama da wata guda ke nan tun bayan da aukuwar rikici a tsakanin Rasha da Ukraine, amma abin bakin ciki shi ne, a yayin da kasar Sin da ma sauran kasashe da dama ke kokarin sulhuntawa a tsakanin kasashen biyu, da ma samar da agajin jin kai ga Ukraine, a hannu guda, Amurka na ci gaba da samar da makamai ga Ukraine, da ma kara kakaba wa Rasha takunkumi, don hura wutar rikicin. (Lubabatu Lei)