logo

HAUSA

An gano gawawwakin dukkanin jami’an wanzar da zaman lafiya 8 da suka yi hadarin jirgin helikwafta a arewacin Kivu

2022-03-30 10:32:01 CMG Hausa

Kakakin babban magatakardar MDD Stephane Dujarric, ya ce an gano daukacin gawawwakin jami’an wanzar da zaman lafiya dake aiki a jamhuriyar dimokaradiyyar Congo ko MONUSCO a takaice, bayan da jirgin helikwaftan da suke ciki ya yi hadari.

Dujarric, ya ce jirgi mai saukar ungulu dauke da jami’an na MONUSCO ya yi hadari ne da safiyar jiya Talata, a kusa da Tshanzu dake kudu maso gabashin lardin Arewacin Kivu, lamarin da ya yi matukar bakanta ran babban magatakardar MDD, sai dai ya ce akwai wasu jami’an dake cikin helikwaftan da suka tsira daga hadarin.

Yanzu haka dai ana gudanar da bincike, domin gano musabbabin aukuwar hadarin. 

Kaza lika Stephane Dujarric ya ce a baya bayan nan, an yi musayar wuta tsakanin mayakan sa kai na M23, da dakarun gwamnatin Congo, a wannan yanki na arewacin Kivu. 

A daya bangaren kuma, rundunar sojojin jamhuriyar dimokaradiyyar Congo, ta ce mayakan M23 ne suka harbo jirgin helikwafan na dakarun MDD, ko da yake MDDr ba ta tabbatar da wannan ikirari ba.   (Saminu)