logo

HAUSA

Kwarewar Sin a yaki da talauci za ta taimakawa kasashe masu tasowa

2022-03-30 09:06:11 CMG Hausa

A wannan makon ne, aka shirya wani taro a Qujing dake lardin Yunnan na kudu maso yammacin kasar Sin, don bitar irin nasarorin da kasar Sin ta cimma a fannin kawar da talauci da raya yankunan karkara. Yayin taron mataimakin firaministan kasar Sin Hu Chunhua ya yi kira da a kara kokarin karfafa nasarorin da aka cimma na yaki da talauci da tabbatar da aiwatar da manufofin da aka tsara na farfado da yankunan karkara domin samun moriya mai kwari.

A cewarsa, ya kamata a kara kudin shigar mutanen da aka fitar daga kangin talauci ya zama jigon aikin, kana a samar da guraben aikin yi da inganta raya masana’antu da kuma kyautata tsarin rayuwar jama’a.

Haka kuma, ya kamata babban burin da za a mayar da hankali kan sa shi ne gaggauta ci gaban gundumomin da suka yaki talauci da kara mayar da hankali kan masana’antun yankunan karkara, A hannu guda kuma yankunan da suka samu ci gaba, su kara zage damtse.

Bugu da kari, mataimakin firaministan ya ce, ya kamata a ingiza farfado da yankunan karkara, kana ya kamata shirin ya shafi dukkan manoma, tare da mayar da hankali kan muhimman bangarori 5 na masana’antu da al’adu da basira da kiyaye muhalli da shirye-shirye.

Masana na ganin cewa, kasar Sin tana dora muhimmanci kan kawar da talauci a cikin yankunan karkara, kuma ta cimma muradun neman ci gaba mai dorewa na MDD ta hanyar amfani da aikin gona na zamani, wannan a cewarsu, wata fasaha ce mai kyau da za ta taimakawa sauran kasashe masu tasowa da ma duniya baki daya. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)