logo

HAUSA

Amurka Mai Son Kakaba Takunkumi Ta Kawo Babbar Illa Ga Duk Fadin Duniya

2022-03-30 21:06:47 CMG HAUSA


Daga Amina Xu

Abokai na, yau “Duniya a zanen MINA” na mai da hankali kan Amurka mai matukar son kakaba takunkumi ga saura. Rahoton da ma’aikatar kudin Amurka ta bayar mai taken “Kimanta takunkumin da Amurka ta sanyawa sauran kasashe a shekarar 2021” na nuna cewa, shekaru 20 da suka gabata, tun barkewar rikicin “9.11”, yawan takunkumin da Amurka ta kakabawa sauran kasashe ya karu matuka. An ce, ya zuwa karshen shekarar 2021, yawan takunkumin da Amurka ta kakkabawa sauran kasashe ya kai fiye da 9400, inda yawansa ya ninka sau 10 bisa na shekaru 20 da suka gabata.

Irin wannan takunkumi tamkar matsin lamba ne ga wasu kasashe marasa karfi, abin da ya haifar da koma bayan tattalin arziki da zaman takewar al’ummarsu. Jaridar “USA TODAY” ta yi hasashen cewa, bayan janyewar sojojin Amurka daga Afghanistan, yawan fararen hula da suka mutu sakamakon takunkumin da Amurka ta kakabawa kasar, ya fi na wadanda suka rasu a cikin yaki na tsawo shekaru 20. Ban da wannan kuma, takunkumin da Amurka ta sanyawa kasashen Iran da Venezuela da sauran kasashe masu arzikin man fetur, ya hana su fitar da man fetur zuwa ketare, matakin da ya sa suka fama da koma bayan tattalin arziki.

Amma shin Amurka ta cimma burinta ta yin amfani da makamin sanya takunkumi? A’a, a hakika wasu kafofin yada labarai a duniya da manazarta sun yi nuni da cewa, amfani da takunkumin da Amurka take sanyawa ya bayyana raguwar karfinta a duniya.

Kakabawa sauran kasashe takunkumi a matsayin wata kasa mafi girma, don tilasta musu durkusawa gabanta mataki ne da ba za a yarda da shi ba, kuma ya kamata kasashe daban-daban sun kara fahimtar juna da cin moriya tare. Ya kamata Amurka ta fahimci wannan ba tare da bata lokaci ba, don tabbatar da zaman lafiya da karko a duniya tun da wuri. Idan wata kasa ta nuna karfin tuwo, ko sanya takunkumi yadda take so don biyan moriyar kashin kanta kawai, to ba bu shakka za a mayar da martani bisa iyakacin kokarinsa. Game da wannan batu, ga Cartoon da na zana. (Mai zane: Amina Xu)