logo

HAUSA

Kasashen Afirka Na Kara Amfana Daga Alakarsu Da Kasar Sin

2022-03-30 21:03:35 CMG HAUSA

Daga Ibrahim Yaya

Tun bayan da shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi bayani game da manufar kasar Sin ga nahiyar Afrika a Tanzania, wadda ta tsara makomar huldar kasashen Sin da Afrika a sabon zamani, wadda yanzu haka ta haifar da kawance da kulla dangantaka da yarda da juna tsakanin bangarorin biyu.

Ita dai wannan manufa da shugaba Xi Jinping ya gabatar, yayin ziyarar farko da ya kai nahiyar Afrika, a matsayinsa na shugaban kasar Sin, a shekarar 2013 ta dogaro ne bisa gaskiya da samun managartan sakamako da fahimtar juna,

Bisa wadannan tsare-tsare, kasar Sin da Afrika, sun hada karfi da karfe, wajen samar da tafarkin samun ci gaba na bai daya, da nufin samar da dangantaka mai karfi da ba a taba ganin irinta ba, tsakanin kasar dake nahiyar Asia da kuma nahiyar Afrika, wadanda yawan al'ummarsu ya kai biliyan 2.5, kwatankwacin daya bisa ukun al'ummar duniya baki daya.

Bayan wadannan shekaru, ana iya ganin dimbin moriyar da aka samu bisa dangantakar dake tsakanin kasar Sin da nahiyar Afrika a fannoni da suka hada da tattalin arziki, da ilimi, da cinikayya, da kayayyakin more rayuwa, da al'adu, da fannin aikin gona, da raya masana'antu da ma kaiwa juna ziyara a bangaren manyan jami'ai da shugabannin sassan biyu.

Tarukan dandalin hadin gwiwar kasar Sin da nahiyar Afrika FOCAC, da suka gudana a birnin Johannesburg na Afrika ta Kudu, da Beijing na kasar Sin da na baya-bayan nan a Dakar na kasar Senegal, gagarumin ci gaba ne ga dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu. Wadanda ke aikewa da muhimmin sako ga al'ummomin duniya cewa, Sin da Afrika sun hada hannu don samun nasara tare.

Sai dai duk da irin wannann ci gaba da sassan biyu suka samu, kasashen yamma sun sha yiwa wannan alaka wata mummunan mahuguwar fahimta, har ma suka nemi bata wannan dangantaka ta fannoni daban-daban. Sai dai bakin alkalami ya riga ya bushe, kuma hakar su ba za ta taba cimma ruwa ba.

Sakamakon wannan hadin gwiwa, kasashen Afrika da Sin, suna kokarin hade manufofi da dabarunsu na samun ci gaba karkashin shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya" da muradun ci gaba masu dorewa na MDD da kuma ajandar raya nahiyar ta kungitar Tarayyar Afrika da ake son cimmawa nan zuwa shekarar 2063. Alakar sassan biyu, tana kara taka muhimmiyar rawa a fannonin inganta rayuwar bil-Adam, matakin da masana suka yaba matuka.

Abubuwa na baya-bayan nan da wasu kasashen Afirka suka amfana da shi daga alakarsu da kasar Sin su ne, kaddamar da babbar gadar Foundiougne mai tsawon mita 1600 da kamfanin kasar Sin ya gina ta hanyar rancen kudin da kasar ta nema daga kasar Sin. Aikin dake zama daya daga cikin manyan ayyukan da ake gudanarwa bisa “shirin farfado da Senegal”, kana ayyukan hadin gwiwa goma karkashin huldar Sin da kasashen Afirka. Sai kuma ginin wata hanya mai tsaown kilomita 100 dake tsakiyar Kumasi, birni mafi girma na biyu a kasar Ghana da sauransu.

Masana na ganin cewa, irin wadannan ayyuka za su inganta da ma saukaka harkokin zirga-zirga, baya ga kara samar da kudaden shiga, matakin da zai kara inganta rayuwar mazauna wuraren. Sin da kasashen Afirka na kara zama tsintsiya madaurinki daya. (Ibrahim Yaya)