logo

HAUSA

Shugaban Ghana ya bude aikin tituna da kamfanin Sin ya gudanar

2022-03-30 14:23:38 CMG Hausa

Shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, a ranar Talata ya jagoranci bude wani gagarumin aikin hanyoyin mota daban-daban wanda kamfanin kasar Sin ya gudanar a Tamale, birni na uku mafi girma a kasar.

Aikin titunan da kamfanin Sinohydro Corporation Limited ya gudanar, wanda ya kunshi manyan hanyoyin mota masu tsawon mita 684, ana sa ran aikin zai taimaka wajen inganta yanayin sufurin ababen hawa a tsakiyar birnin.

Da yake yanka kyalle a bikin bude aikin, Akufo-Addo, ya yabawa aikin bisa yadda ya samar da muhimmiyar damar kyautata yanayin sufurin birnin domin amfanin al’ummar kasar Ghana. Yana mai cewa, aikin tamkar wani kyakkyawan misali ne dake alamta kyawun alakar dake tsakanin Ghana da Sin.

Lu Kun, jakadan kasar Sin a Ghana, ya bayyana farin cikinsa ga kamfanin na kasar Sin, saboda muhimman ayyukan da ya gudanar cikin shekaru ukun da suka gabata duk da irin kalubalolin da annobar COVID-19 ta haifar, sannan ya yaba da goyon bayan da gwamnnatin Ghanan ke bayarwa.

Jakadan na Sin ya bayyana aikin a matsayin wani muhimmin ci gaba a tarihin hadin gwiwar Sin da Ghana. Yana mai cewa, gwamnatin kasar Sin ta himmatu matuka wajen tabbatar da ci gaban tattalin arzikin Ghana, da kyautata zaman rayuwar al’ummar Ghana, a shekaru da dama ta hanyoyi daban-daban. (Ahmad)